Mun gaza, ku yafe mana - Sanata Giwa a kan guiwa tana bai wa matasa hakuri (Bidiyo)

Mun gaza, ku yafe mana - Sanata Giwa a kan guiwa tana bai wa matasa hakuri (Bidiyo)

- Sanata Florence Ita-Giwa ta gurfana a kan guiwoyinta tana rokon fusatattun matasa a Calabar

- Kamar yadda bidiyon ya bayyana, ta amince da cewa shugabanni a Najeriya sun gaza

- Ta bukaci matasan da su dauka hakuri a kan abinda ke faruwa a kasarsu, su daina rikicin

Tsohuwar mai bada shawara ta musamman a kan al'amuran majalisar dattawa, Sanata Florence Ita-Giwa, ta gurfana a kan guiwoyinta inda take rokon matasa da su daina kwashe musu kadarori a Calabar.

Ta yi wannan kiran ne a ranar Asabar, inda ta amince da cewa shugabannin sun gaza kuma sun ci amanar matasa, Channels TV ta wallafa.

Kamar yadda tsohuwar sanatar ta sanar, lalata kadarori tare da haddasa rikici da ake yi yanzu kawai yana shafar masu kudi ne amma talakawa suna rayuwarsu lafiya kalau.

"Ina rokon ku 'ya'yana, mun san cewa mun gaza kuma mun yi kuskure. Kasar ku Najeriya ta gaza kuma shugabannin sun kasa tsayar da wannan rikicin," tace.

A tun farko, gwamnan jihar Farfesa Ben Ayade ya saka dokar ta baci na sa'o'i 24 domin dakile rikicin da ya hada da wasu sasaan jihar.

Kamar yadda takardar da ta fita a ranar Juma'a ta nuna cewa dokar ta bacin za ta fara ne a take.

Wannan cigaban kamar yadda takardar ta bayyana, an tabbatar da ita ne domin rikicin da zanga-zangar ta koma a fadin jihar.

A yayin bai wa jama'ar jihar shawara, Ita ta ja kunnen jami'an tsaron da su damke duk wanda ya take dokar.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: 'Yan sanda sun halaka mutum 6 da ake zargin 'yan Boko Haram ne

Mun gaza, ku yafe mana - Sanata Giwa a kan guiwa tana bai wa matasa hakuri (Bidiyo)
Mun gaza, ku yafe mana - Sanata Giwa a kan guiwa tana bai wa matasa hakuri (Bidiyo). Hoto daga @ChannelsTv
Asali: Twitter

KU KARANTA: Shugabanni su farka, mulkin kama-karya ne yake fusata matasa - Okorocha

A wani labari na daban, Zanga-zangar EndSARS ta canja salo cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, jaridar The Nation ta wallafa.

A jawabin da shugaban kasa yayi da daren Alhamis, wanda ya ja kunnen wadanda suka yi uwa da makarbiya a kan zanga-zangar ya ce lallai gwamnatin tarayya ba za ta yarda da sauran ta'addanci ba.

Yace: "Wajibi ne in ja kunnen wadanda suka canja wa zanga-zangar EndSARS salo daga asalin makasudinta, wadda matasa suka fara a kan dakatar da rundunar SARS."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel