Sojin saman Najeriya sun kai samame, sun halaka 'yan Boko Haram masu yawa a Borno

Sojin saman Najeriya sun kai samame, sun halaka 'yan Boko Haram masu yawa a Borno

- Rundunar sojin saman Najeriya na cigaba da samun manyan nasarori a yankin arewa maso gabas

- Sun yi nasarar kai samame ta jiragen yaki inda suka tarwatsa maboya tare da wasu 'yan ta'addan

- Rundunar Operation Wutar Tabki ta kai samamen a Ngwuri Gana da ke kusa da Gulumba Gana-Kumshe a Borno

Mayakan ta'addancin Boko Haram masu tarin yawa sun sheka lahira a Ngwuri Gana da ke Junacheri a jihar Borno bayan ragargazar da aka yi musu ta jiragen yaki a maboyarsu.

A wata takarda sa shugaban fannin yadaabarai na rundunar soji, Manjo Jabar John Enenche ya fitar, ya ce hakan na daga cikin kakkabar da suke yi wa 'yan ta'adda a yankin arewa maso gabas.

KARANTA WANNAN: Gwamna AbdulRazaq ya bai wa 'yan kasuwar da suka yi asara N500m

Sojin saman Najeriya sun kai samame, sun halaka 'yan Boko Haram masu yawa a Borno
Sojin saman Najeriya sun kai samame, sun halaka 'yan Boko Haram masu yawa a Borno - @thenationnews
Asali: Twitter

Kamar yadda yace: "Muna cigaba da matsantawa 'yan ta'adda a yankin arewa maso gabas na kasar nan karkashin Operation Wutar Tabki.

"A irin haka ne, rundunar Operation Lafiya Dole ta tarwatsa maboyar 'yan ta'adda tare da kashe masu tarin yawa a Ngwuri Gana da ke kusa da Gulumba Gana-Kumshe a Borno.

KARANTA WANNAN: Dalilin da yasa Buhari ya ki magana a kan harbin Lekki - Fadar shugaban kasa

"An samu wannan basarar ne bayan samame mabanbanta da aka kai a ranar 21 da 22 ga watan Oktoban 2020 bayan bayanan sirri da aka samu.

"Bayan bincike, mun tabbatar da cewa akwai wurare biyu da 'yan ta'addan ke buya, don shirya duk wani ta'addancin su.

"Dakarun sojin sun ragargaza maboyar tare da kashe 'yan ta'addan masu yawa," a cewar sa.

A wani labarin, wasu mutane da ake zargin 'yan daba suka tsinke kan dan sanda tare da kone shi kurmus yayin zanga-zangar EndSARS a Nnewi da ke jihar Anambra.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Haruna Mohammed, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce wasu 'yan sandan uku sun samu miyagun raunika.

Ya ce an gaggauta mikasu asibiti domin samun taimakon likitoci na gaggawa, The Nation ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel