EndSARS: Obasanjo ya jinjina wa jawabin Shugaba Buhari kan zanga-zangar EndSARS

EndSARS: Obasanjo ya jinjina wa jawabin Shugaba Buhari kan zanga-zangar EndSARS

- Cif Olusegun Obasanjo ya yaba ma Shugaban kasa Buhari kan gane cewa yan Najeriya na da yancin yin zanga-zangar lumana

- Tsohon Shugaban kasar ya jinjinawa Buhari a kan jawabin da ya yiwa kasar a yayinda ake tsaka da tashin hankali sakamakon zanga-zangar EndSARS

- Shugaba Buhari ya karbi bakuncin dukkanin tsoffin shugabannin kasar Najeriya da ke raye a ranar Juma’a kan halin da kasar ke ciki

Cif Olusegun Obasanjo ya yaba ma Shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan jawabin kasa da yayi kan zanga-zangar EndSARS.

Tsohon shugaban kasar ya kasance daya daga cikin shugabannin Najeriya da ke raye wadanda Buhari ya gayyata zuwa wani taro na yanar gizo a ranar Juma’a, 23 ga watan Oktoba.

Da yake magana a wajen taron, Obasanjo ya yaba ma Shugaban kasa Buhari a kan nunawa da yayi cewa zanga-zangar lumana na daga cikin damokradiyyar Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Mutum 5 sun mutu yayin rabon kuɗin da suka tsinnta a ma'ajiyar kayan tallafin korona

EndSARS: Obasanjo ya jinjina wa jawabin Shugaba Buhari kan zanga-zangar EndSARS
EndSARS: Obasanjo ya jinjina wa jawabin Shugaba Buhari kan zanga-zangar EndSARS Hoto: @DailyPostNGR
Asali: Twitter

Legit.ng ta tuna cewa Shugaban kasar ya yi jawabi ga yan Najeriya a yammacin ranar Alhamis, 22 ga watan Oktoba, a yayinda ake tsaka da zanga-zangar neman shugabanci nagari da kawo karshen cin zalin yan sanda.

KU KARANTA KUMA: ENDSARS: 'Yan daba sun kai farmaki ofisoshin NLC, INEC, SEMA da wasu hukumomi a Calabar

A jawabin nasa, Shugaban kasar ya dakatar da zanga-zangar EndSARS sannan ya bayar da tabbacin cewa za a biya wa masu zanga-zangar bukatunsu.

Daga bisani Buhari ya karbi bakuncin dukkanin tsoffin shugabannin Najeriya da suka hada da Goodluck Jonathan, Obasanjo da sauransu domin sanar da su halin da kasar ke ciki.

Da yake magana a taron, Obasanjo, wanda ya bayyana cewa “kasar na ta jira” ya ce ya yi farin ciki da ganin cewar an amshi bukatun masu zanga-zanga.

“Na yaba da jawabin daren jiya. Kasar na ta jira. Ka yi zantuka masu ma’ana da suka cancanci yabo.

“Zanga-zangar lumana na daga cikin koyarwar damokradiyya. An amshi bukatun masu zanga-zanga na akika, kuma kana aiki a kan aiwatar da su. Mun jinjina maka.”

A gefe guda, Ma'aikatar Shari'ar jihar Legas za ta hukunta mutane 229 da yan sanda suka damke da zargin amfani da zanga-zangan EndSARS wajen lalaci, da fashin dukiyoyin gwamnati da na mutane masu zaman kansu.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ta samu jawabin daga Diraktan labaran ma'aikatar, Mr Kayode Oyekanmi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel