Abin ya isa haka, kowa ya shiga taitayinshi - IGP ya baza manyan yan sanda gari

Abin ya isa haka, kowa ya shiga taitayinshi - IGP ya baza manyan yan sanda gari

- Bayan kwanaki 3 jere kowa na cin karansa ba babbaka, IGP ya ce abin ya isa

- Ya umurci kwamishanonin yan sanda su dakile duk wanda ya ke son cigaba

- Cikin kwanakin nan, an fasa shagunan mutane suna satan kayayyaki

Sifeto Janar na yan sanda, IGP Mohammed Adamu ya bada umurnin tura jami'an yan sanda domin kawo karshen lalata, sace-sacen da kashe-kashen da ake yi a fadin tarayya.

Ya bada umurnin ne ga dukkan mataimakan Sifeto AIG, Kwamishanoni, kwamandoji da masu yaki da ta'addanci.

Kakakin hukumar yan sanda, Frank Mba, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Asabar, a birnin Abuja .

Adamu ya umurci manyan jami'an yan sanda su tabbatar da cewa kowa ya shiga taitayinsa.

Musamman ya umurci kwamishanoni da shugabannin rundunonu su tura jami'ansu wuraren da suke shugabanta domin tabbatar da zaman lafiya.

KU KARANTA: Matasa sun kai farmaki dakin ajiyan kayan talafin Korona, sun debi buhuhunan hatsi

Abin ya isa haka, kowa ya shiga taitayinshi - IGP ya baza manyan yan sanda gari
Abin ya isa haka, kowa ya shiga taitayinshi - IGP ya baza manyan yan sanda gari
Asali: Twitter

Shugaban yan sandan ya yi kira ga mutan Najeriya masu bin doka kada su tayar da hankali amma su hada kai da yan sanda wajen kare dukiyoyin al'umma.

Ya gargadi masu tayar da zaune tsaye suyi hattara saboda ba za'a sake lamuntan abubuwan da suke yi na saba doka ba.

KU KARANTA: Matasan sun yi cincirindo a Jos domin diban kayan tallafin Korona (Bidiyoyi)

Bayan harbin matasa masu zanga-zangan da Sojoji sukayi a daren Talata a Lekki Toll Gate, bata gari sun bazama cikin gari suna fasa ofishohin gwamnati, shagunan jama'a, kone-kone kamfanoni da tare mutane a hanya suna karba kudi.

Daga baya gama garin jama'a suka fara fasa dakunan ajiyan kayan tallafin Korona na hatsi suna kwasa a jihohin daban-daban.

Daga jihohin da akayi wawason kayan tallafin Korona sune Legas, Plateau, Kwara, Cross River, Osun dss.

Kawo yanzu an damke mutane 229 da ake zargi da lalata a jihar Legas.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel