Kalaman Fafaroma Francis a kan auren jinsi zasu jawo ma sa suka a duniya

Kalaman Fafaroma Francis a kan auren jinsi zasu jawo ma sa suka a duniya

- Shugaban darikar Katolika, Fafaroma Francis, ya bayyana goyon bayansa ga dokokin kare hakkin ma su auren jinsi

- Ma su nazarin al'amura sun bayyana cewa kalaman Fafaroma Francis zasu jawo masa caccaka a duniya

- Fafaroma Francis ya dade yana goyon bayan auren jinsi duk da har yanzu ya na kyamar luwadi

Fafaroma Francis, shugaban mabiya darikar Katolika a addinin Kirista, ya furta Kalaman nuna goyon bayan ma su auren jinsi.

Yayin da ya ke jawabi a wani shirin gidan talabijin mai taken 'Francesco', wanda aka nuna a birnin Rome na kasar Italy, Fafaroma Francis ya goyi bayan dokokin kare hakkin ma su auren jinsi.

A cewar Fafaroma Francis, ma su sha'awar auren jinsi na 'yancin kasancewa tare, a saboda haka bai kamata a saka rayuwarsu cikin garari ba.

Ana ganin cewa Kalaman Fafaroma Francis zasu jawo masa caccaka daga masu ra'ayin rikau da masu kyamar auren jinsi, kamar yadda wakilin BBC ya bayyana.

KARANTA: Rundunar soji ta kama sojan da ke goyon bayan ma su zanga-zanga

Tun kafin hawansa karagar Fafaroma, Francis ya kasance mai goyon bayan auren jinsi duk da har yanzu bai daina adawa da 'yan luwadi ba.

Kimanin sati biyu da suka wuce ne Fafaroma Francis ya ce shugaban kasar Amurka, "Donald Trump ba kirista bane."

Suna da ikon kasancewa tare, kar a tsangwamesu - Kalaman Fafaroma kan auren jinsi
Fafaroma Francis
Asali: Twitter

Ya bayyana hakan ne yayin da ya ke mayar da martani a kan alkawarin da Trump ya dauka cewa zai kori bakin 'yan gudun hijira daga Amurka tare da tilasta kasar Mexico biyan kudin gina Katanga a iyakarta da Amurka.

KARANTA: A karshe: Buhari ya magantu kan zanga-zangar #EndSARS, ya roki wata alfarma wurin matasa

"Duk wani mutum da ke tunanin gina katanga, ba gina gada ba, ba kirista bane," kamar yadda Fafaroma ya fada yayin amsa tambayar dan jarida a birnin Rome na kasar Italy bayan dawowarsa daga wata ziyara ta kwana 6 a kasar Mexico.

"Ba zan shiga batun siyasa ba," Fafaroma ya fada a matsayin amsar tambayar ko zai shawarci mabiya Cocin Katolika a kan dan takarar da ya kamata su zaba a kasar Amurka.

Fafaroma Francis ya cigaba da cewa; "abinda na fada shine cewa Shi (Trump) ba Kirista bane matukar ya furta hakan."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel