Tura ta kai bango, idon matasa ya bude - ACF ta gargadi shugabanni

Tura ta kai bango, idon matasa ya bude - ACF ta gargadi shugabanni

- Kimamnin sati biyu kenan da matasa suka fara zanga-zangar neman a rushe rundunar SARS, sannan a yi rundunar 'yan sanda garambawul

- Duk wata barazana da lallabi ya gaza yin tasiri wajen shawo kan fusatattun matasa da ke zanga-zanga a sassan Najeriya

- Jama'a na ganin cewa zanga-zangar na kara yin karfi ne saboda matasa Najeriya sun dade suna jin haushin burus dasu da matsalolinsu da mahukunta ke yi

Ƙungiyar tuntuba da cigaban Arewa (ACF) a ranar Laraba ta yi gargaɗin cewa ya kamata shugabannin Najeriya sun sani ba za su cigaba da yin burus da matasa da kuma buƙatunsu ba.

ACF ta bayyana cewa cigaba da yin burus da bukatun matasa tare da matsalolinsu kan iya janyo gagarumar matsala a kasa.

Shugaban ƙungiyar ACF, Audu Ogbeh, ne ya bayyana hakan a wani taron tattaunawa na manyan shugabannin al-umma na ƙasa da aka yi a Kaduna.

"Halin da ake ciki na zullumi da fargaba musamman a arewacin ƙasar nan babbar barazana ce ga zaman lafiya da cigaban yankin da kuma ƙasa baki ɗaya," a cewar Ogbeh, tsohon ministan noma a zangon mulkin Buhari na farko.

KARANTA: Bidiyo: Rundunar soji ta kama sojan da ke goyon bayan ma su zanga-zanga

Kalaman na Ogbeh sun zo ne a kan gaɓar hargitsi da ake fama dashi a wasu jihohi a ƙasar nan bayan matasa sun shafe kusan mako biyu suna gudanar da zanga-zanga don ganin sun kawo ƙarshen zaluncin ƴansanda.

Ogbeh ya ce a halin da ake ciki, akwai buƙatar shugabanni su sauya salo da dabaru, sannan su maida hankali a kan cigaban kasa musamman inda muke fuskantar ƙalubale da suka shafi ɓangarorin siyasa, tattalin arziƙi da kuma zamantakewa.

Tura ta kai bango, idon matasa ya bude - ACF ta gargadi shugabanni
Audu Ogbeh
Asali: Depositphotos

"Za mu iya, kuma dole mu fuskanci abin da yake gabanmu ta hanyar zuba hannun jari a harkar ilmi, noma da kiwo da kuma masana'antu.

"Dole ne mu tafi da matasa, wadanda dama ƴaƴanmu ne, sannan mu haɗa hannu da su, mu tallafa musu, har ma mu koya daga garesu.

DUBA WANNAN: Ganduje ya dauki matakin dakatar da zanga-zanga a Kano bayan an kama farar hula da bindiga, an kone motoci

Lokaci ya wuce da zamu yi burus dasu da buƙatunsu. Yin burus da matasa tamkar mun daɓawa kan mu wuƙa ne," a cewarsa.

Shugaban na ACF ya ƙara da cewa; "halin zullumi da fargaba na matasa musamman a arewacin Najeriya babbar barazana ce ga yankin da kuma ƙasa baki ɗaya."

"Ina sa ran cewa yanzu, fiye da lokutan baya, shine lokacin da masu ruwa da tsaki za su saka hannu don a magance matsalolin kasa da kuma ceto makomar yaranmu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel