Da duminsa: IGP ya janye 'yan sanda masu tsaron dukkan manyan mutane a Najeriya

Da duminsa: IGP ya janye 'yan sanda masu tsaron dukkan manyan mutane a Najeriya

- Shugaban 'yan sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu, ya bada umarnin janye 'yan sanda masu kare lafiya

- Ya umarci janye dukkan 'yan sandan da ke tsaron lafiyar manyan mutane a fadin Najeriya a yau Laraba

- Gidajen gwamnatoci, shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai kadai aka amince a basu kariya

Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya IGP Mohammed Adamu, ya bada umarnin janye dukkan 'yan sandan da ke tsaron lafiyar manyan mutane a fadin kasar nan.

Kamar yadda aka gano, wannan hukuncin ya biyo bayan bukatar sake assasa dokar dakile zanga-zangar EndSARS a tituna.

Wannan umarnin na kunshe ne a wani sako da aka mika ga dukkan kwamandojin 'yan sandan kasar nan a ranar Litinin wanda jaridar The Cable ta gani.

A umarnin, wanda zai fara aiki a take, gidajen gwamnati, shugaban majalisar dattawa da kuma kakakin majalisar wakilai ne aka tsame.

"Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya ya bada umarnin janye dukkan 'yan sandan da ke tsaron manyan mutane banda na gidajen gwamnati, shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai," sakon yace.

"Duk wani kwamandan da ya saba wannan dokar zai fuskanci hukunci. Duk wani jami'in tsaro da aka kama yana tsaron wani babban mutum da makami ko babu, za a sauya masa wurin aiki kuma za a hukunta kwamandansa."

An umarci dukkan 'yan sanda masu tsaron da aka janye da su gaggauta zuwa gaban kwamandansu.

KU KARANTA: Hotunan kyawawan gidaje 7 na miliyoyin daloli mallakin Donald Trump

Da duminsa: IGP ya janye 'yan sanda masu tsaron dukkan manyan mutane a Najeriya
Da duminsa: IGP ya janye 'yan sanda masu tsaron dukkan manyan mutane a Najeriya. Hoto daga @Dailynigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Za mu cigaba da matsanta wa masu laifin da ke barazana ga tsaron kasa - FG

A wani labari na daban, Bata-garin matasa a ranar Laraba sun banka wa gidan iyayen gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, wuta.

Gidan yana kan titin Omididun inda suka dinga jifansu da duwatsu. Gwamna Sanwo-Olu ya saka dokar ta baci ta sa'o'i 24 a jihar sakamakon zanga-zangar EndSARS a ranar Talata.

Daga bisani sojoji sun shiga lamarin, abinda ya kawo mutuwar a kalla mutane 7 wadanda da yawansu matasa ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel