'Kune fa manyan gobe'; Bidiyon yadda sojoji su ka kwantar da murya don lallaba ma su zanga-zanga

'Kune fa manyan gobe'; Bidiyon yadda sojoji su ka kwantar da murya don lallaba ma su zanga-zanga

- A daren ranar Talata ne kafafen yada labarai da dandalin sada zumunta su ka zargi rundunar soji da budewa ma su zanga-zanga wuta a Legas

- Sai dai, rundunar soji ta musanta rahotannin tare da bayyana cewa ba ta aika dakarunta wurin zanga-zangar

- Wasu dakarun soji da suka fita domin kare masana'antu da gine-ginen gwamnati ranar Laraba sun fara lallaba matasan da ke zanga-zanga a Lagos da Osun

A cikin wani faifan bidiyo da ya yi farin jini a dandalin sada zumunta, an ga sojojin Najeriya na lallaba matasa ma su zanga-zanga a jihar Legas.

A daren ranar Talata ne wasu kafafen yada labari na gida da ketare suka wallafa rahoton cewa dakarun soji sun budewa ma su zanga-zanga a yankin Lekki na jihar Legas wuta.

Sai dai, a cikin faifan bidiyon da aka nada ranar Laraba yayin zanga-zanga a jihar Legas, an ji sojoji suna huduba cikin lafazi mai dadi ga matasan da ke zanga-zanga.

KARANTA: A karshe: Buhari ya magantu a kan zanga-zangar ENDSARS, ya fadi bukatarsa wurin matasa cikin lafazi mai sanyi

''Kune fa manyan gobe, mun zo nan wurin ne saboda ku, mun zo domin mu baku kariya, mun zo ne domin kare rayuka da dukiyoyi.

"Akwai batagari da suka shiga cikinku, su muke nema domin fitar dasu daga cikinku, mun san ma su zanga-zanga na gaske, mun san kuma ma su laifi," kamar yadda wani soja ke fada a cikin faifan bidiyon

Kazalika, wasu matasa ma su zanga a Osogbo, jihar Osun, sun yi murna ranar Laraba bayan sojoji sun basu karfin gwuiwa yayin da su ke cigaba da zanga-zanga duk da an saka dokar hana fita.

KARANTA: Bidiyo: Rundunar soji ta kama sojan da ke goyon bayan ma su zanga-zanga

Sojojin sun yi magana da matasan cikin lafazi mai dadi inda suka fadar dasu cewa sune shugabannin gobe, a saboda haka akwai bukatar su gabatar da korafe-korafensu cikin lumana.

'Kune fa manyan gobe'; Bidiyon yadda sojoji su ka kwantar da murya don lallaba ma su zanga-zanga
Sojojin Najeriya
Asali: UGC

"Dukkanmu muna son gobenmu ta yi kyau, amma ba zamu samu hakan ba ta hanyar tashin hankali. Ya kamata mu natsu, mu nemi hakkinmu cikin zaman lafiya," a cewar jagoran sojoji.

Kalaman sojan sun sa matasa barkewa da tafi da shewar jinjina domin nuna jin dadinsu da lafazin sojan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel