Tabarbarewar Najeriya: Buhari ya dora laifi a kan Obasanjo, Yar'Adua da Jonathan

Tabarbarewar Najeriya: Buhari ya dora laifi a kan Obasanjo, Yar'Adua da Jonathan

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dora laifin tabarbarewar kasar a kan shugabannin baya

- Koda dai Buhari bai kama suna ba, ya ce shugabannin da suka mulki kasar tsakanin 1999 zuwa 2015 sun kusa rusa kasar

- Ya kuma ce wadannan mutane ne ke yunkurin caccakar kokarin gwamnatinsa a yanzu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 1 ga watan Okotoba, ya dora laifin halin da kasar ke ciki a kan shugabannin Najeriya da suka gabata, ya ce sun “kusa rusa kasar.”

Koda dai Shugaban kasar bai ambaci sunan shugabannin ba, ya yi hannunka mai sanda ga wadanda suka mulki Najeriya a tsakanin 1999 da 2015, inda ya dasa ayar tambaya kan yadda aka yi har shugabannin suke da bakin sukar gwamnatinsa.

“Wadanda suka yi mulki daga 1999-2015, wadanda suka kusa durkusar da kasar a yanzu sune suke yunkurin sukar kokarinmu."

KU KARANTA KUMA: Nigeria @ 60: Muhimman abubuwa 7 a jawabin Buhari

Shugabannin Najeriya tun daga 1999 sune Olusegun Obasanjo (1999 zuwz 2007), Marigayi Umaru Yar’Adua (2007 zuwa 2010), Goodluck Jonathan (2010 zuwa 2015).

Tabarbarewar Najeriya: Buhari ya dora laifi a kan Obasanjo, Yar'Adua da Jonathan
Tabarbarewar Najeriya: Buhari ya dora laifi a kan Obasanjo, Yar'Adua da Jonathan Hoto: Naija News
Asali: UGC

Jawabin na ranar Alhamis ya kasance karo na farko da shugaba Buhari ke martani da kansa tun bayan sukar gwamnatinsa da Obasanjo yayi a baya-bayan nan.

Jaridar Premium Times ta ruwaito yadda Obasanjo ya yi korafi a kan tabarbarewar tsaro da kuma halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, inda ya daura laifin a kan gwamnatin Buhari.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya tabbatar da tabarbarewar tattalin arziki da tsaro a Najeriya

A gefe guda, tsohon Shugaban hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega na so a ga abubuwan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadi a jawabinsa na ranar yancin kai a kasa, ba wai ya tsaya a fatar baki ba kawai.

Tsohon Shugaban na INEC ya yi magana ne a ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoba, a lokacin wani shiri na musamman na gidan talbijin din Channels.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel