Nigeria @ 60: Muhimman abubuwa 7 a jawabin Buhari

Nigeria @ 60: Muhimman abubuwa 7 a jawabin Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jawabi ga 'yan Najeriya a cikar kasar shekaru 60 da samun 'yancin kai

- Daga cikin jawabinsa, akwai abubuwa bakwai da ya yi bayani mai zurfi a kai

- Ya yi godiya ga 'yan Najeriya da suka amince da shi tare da fatan samun Najeriyar fiye da ta da

Ga muhimman abubuwa bakwai masu muhimmanci da Shugaba Buhari yayi magana a kai:

1. Dole ne a daidaita farashin man fetur. A halin yanzu muna siyar da litar man fetur N161 wanda hakan sauki ne a kan sauran kasashen duniya.

2. Kasar Masar suna siyar da litar man fetur N211, Saudi Arabia tana siyarwa a N168,, babu ma'ana kasar Najeriya ta cigaba da siyarwa kasa da su.

3. Najeriya tana da matasa miliyan 45 kuma masu zama a birane suna kai miliyan 7 inda suka mamaye fadin 910,768SqKm

4. Najeriya tana da yawan mutane da suka zarce miliyan 200 kuma kashi 52 daga ciki suna zama a birane.

5. Domin samun kasar da muke bukata, dole ne mu mayar da hankali wurin shawo kan kalubalen da suka addabemu.

6. hadin kai babban lamari ne ga 'yan Najeriya, dole ne mu inganta zaman lafiya, tsaro da hadin kan kasar nan.

7. Babu gwamnati da ta shude wacce ta iya abinda muka yi. Gwamnatocin da suka gabata, daga 1999 zuwa 2015 a halin yanzu su suke caccakar kokarinmu.

KU KARANTA: 'Yan Najeriya za su yi alfahari da Buhari a kan kokarinsa a fannin wutar lantarki - Saleh Mamman

Nigeria @ 60: Muhimman abubuwa 7 a jawabin Buhari
Nigeria @ 60: Muhimman abubuwa 7 a jawabin Buhari. Hoto daga @Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: Mutum na farko da ya warke daga cutar HIV ya rasu sakamakon cutar Cancer

A wani labari na daban, mai girma, Sarauniyar Ingila ta turo sakon taya murna ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan bikin murnar cikar Najeriya shekaru 60 da samun 'yancin kai da za'ayi ranar 1 ga watan Oktoba, 2020.

Mai bai wa Shugaban kasa shawara akan harkokin yada labarai, Chief Femi Adesina ne ya sanar da hakan a wata takardar da ya bayar ranar Laraba a Abuja, inda yace hukumar Birtaniya dake Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel