EFCC ta ce ‘Dan kwangilar karya zai yi zaman gidan yari na shekara 125

EFCC ta ce ‘Dan kwangilar karya zai yi zaman gidan yari na shekara 125

- Kotu ta samu wani mutumi da laifin karbar kwangilar karya a Jihar Borno

- EFCC ta ce Alkali ta yankewa Allen Abel jimillar daurin shekaru sama da 100

- Wannan mutumi zai maidawa kamfanoni dukiyar da ya karba a hannunsu

Wata babban kotun jihar Borno da ke zama a garin Maiduguri, ta yankewa wani mutumi mai suna Allen Abel, dogon dauri a gidan kurkuku.

Mista Allen Abel zai shafe shekaru 125 a gidan maza bayan kotu ta same shi da laifin karbar kwangilar karya na kawo kayan abinci.

The ICIR ta ce wannan mutumi ya karbi kwangilar karya ta cewa zai shigo da buhunan shinkafa da kwalayen taliya har na N12, 879,800.

Mai magana da yawun bakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya shaidawa ICIR wannan jiya.

KU KARANTA: Miyagu sun aukawa Fulani a Ebonyi sun yi kisa, raunata wasu

Wannan mutumi ya karbo kwangilar karyar ne da sunan ma’aikatar bada tallafi da agajin gaggawa a karkashin tsarin ciyar da ‘yan makaranta.

EFCC ta gurfanar da Abel a gaban Alkali mai shari’a, Aisha Kumaliya tare da wasu; Suleiman Adamu, Usman Adamu da Kingsley Madubuagu.

Zargi 20 da ake yi wa Abel da sauran mutane uku sun hada da mallakar takardun karya da kuma amfani da sunan wani ta hanyar shaidar karya.

Mai magana a madadin EFCC ya ce an samu Abel da laifin karbar kwangilar karya ta buhuna 480 na shinkafa da kwalaye 1313 na taliya a kan miliyan 12.

EFCC ta ce ‘Dan kwangilar karya zai yi zaman gidan yari na shekara 125
Mr. Allen Abel Hoto: ICRI
Asali: UGC

KU KARANTA: Alkali ya yankewa 'Dan Yahoo-Yahoo dauri a gidan kaso

Wannan mutumi ya karbi kayan abincin ne daga Lelle Hyelwa Sini na kamfanin Lelle Foresight Construction Co. Ltd da sunan gwamnatin tarayya.

A karshe an yankewa Abel daurin shekaru bakwai, biyar, biyar da sauransu. Kuma zai biya kamfaonin Lele Foresight da Lele Foresight kudinsu.

Idan za ku iya tunawa, a shekarar nan ne Kotu ta yankewa tsohon kakakin PDP na kasa, Olisah Metuh hukuncin daurin shekaru 39 a gidan yari.

Alkali Okon Abang ya zartar da hukuncin a kan Metuh bayan an same shi da laifin almundahana.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel