Dan majalisar PDP tilo na jihar Yobe ya sauya sheka zuwa APC

Dan majalisar PDP tilo na jihar Yobe ya sauya sheka zuwa APC

- Dan majalisar jihar Yobe mai wakiltar mazabar Nuguru ta tsakiya, Lawan Inuwa ya fice daga PDP ya koma APC

- Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya tarbe shi a gidan gwamnati a ranar Laraba inda ya yaba masa kan matakin da ya dauka

- Gwamna Buni ya bukaci dukkan sauran 'ya'yan jam'iyyar APC na jihar su rungume shi su bashi dukkan goyon bayan da ya ke bukata

Mista Lawan Inuwa, dan majalisar Jam'iyyar PDP guda daya tak a majalisar jihar Yobe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress, APC.

Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya tarbe shi a gidan gwamnatin jihar da ke Damaturu a ranar Laraba kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Dan majalisar PDP tilo na jihar Yobe sauya sheka zuwa APC
Dan majalisar PDP tilo na jihar Yobe sauya sheka zuwa APC. Hoto @360nobs
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotuna: 'Yan sanda sun yi holen 'yan fashi da makami da masu garkuwa a Abuja

Inuwa dan asalin karamar hukumar Nguru ne kuma yana wakiltar mazabar Nguru ta tsakiya ne a Majalisar Jihar ta Yobe.

Shugaban jam'iyyar APC na jihar, Alhaji Adamu Chilariye da sakataren jam'iyyar Alhaji Abubakar Bakabe ne suka masa rakiya zuwa ganawarsa da gwamnan.

Buni ya yi maraba da dan majalisar jihar da yace dama gida ya dawo kuma sun dade suna tattaunawa.

KU KARANTA: 'Ka gayyato sojojin Chadi su taya mu yaki da Boko Haram' - Zulum ya roki Buhari

Gwamna Buni ya yabawa dan majalisar kan dawowa jam'iyyar ta APC da yace al'ummar mazabarsa suna goyon bayan hakan.

Gwamnan ya bukaci masu ruwa da tsaki a Nguru su rungumi Nguru Lawan hannu biyu-biyu inda ya ce jam'iyyar APC a Yobe dukkansu tsintsiya ce madaurinki daya kuma suna taimakawa juna.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, kun ji shugaban jam'iyyar Social Democratic Party, SDP, na kasa Farfesa Tunde Adeniran a ranar Talata ya sanar da cewa ya yi murabus daga harkokin siyasa ta hammaya.

Adeniran ya sanar da hakan ne cikin wata wasika mai dauke da sa hannunsa da kwanan watan 29 ga watan Satumban 2020 da ya aike wa hedkwatan jam'iyyar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel