Makiyaya sun mutu a harin da aka kai wa rugar Fulani a Ebonyi inji ‘Yan Sanda

Makiyaya sun mutu a harin da aka kai wa rugar Fulani a Ebonyi inji ‘Yan Sanda

- A ranar Litinin aka kai wa rugar Fulani hari a dajin Ukwu-Achi Ishieke

- ‘Yan Sanda sun tabbatar da cewa an kashe Makiyaya, an raunata wasu

- Kwamishina ya ce sun fara binciken harin domin a hukunta masu laifin

Akalla mutum biyu ake zargin cewa sun rasu a kauyen Ukwu-Achi Ishieke da ke karamar hukumar Ebonyi, jihar Ebonyi a sakamakon wani hari.

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto a ranar 29 ga watan Satumba, 2020, cewa wasu miyagu da ba a sansu ba, sun aukawa makiyaya har sun kashe su.

Ana zargin cewa wannan rikici bai rasa alaka da sabanin da ake samu da makiyaya a kasar nan.

Binciken da jaridar ta yi ya nuna cewa mazauna yankin da abin ya faru su na wasan bere da jami’an tsaro saboda tsoron jami’an ‘yan sanda su cafke su.

KU KARANTA: Yadda wasu Makiyaya su ka yi ta'adi a Jigawa

Wannan kauye na Ukwu-Achi Ishieke da abin ya faru, ya na kan titin garin Enugu ne zuwa Abakaliki.

Da aka tuntubi mai magana da yawun ‘yan sanda na jihar Ebonyi, DSP Loveth Odah, ta shaidawa ‘yan jarida ba su da cikakkiyar masaniya kan lamarin.

DSP Loveth Odah ta yi alkawarin za ta sanar da manema labarai halin da ake ciki daga baya.

“Ba ni da bayani game da sabanin, amma ni da kwamishinan ‘yan sanda mu na shirin zuwa wurin domin mu ganewa idanunmu abin da ya faru.” Inji Odah.

KU KARANTA: Turakin Zazzau ya dawo cikin lissafi a tseren sarautar Zazzau

Makiyaya sun mutu a harin da aka kai wa rugar Fulani a Ebonyi inji ‘Yan Sanda
Makiyaya Hoto: The Guardian
Asali: UGC

A gefe guda, kwamishinan ‘yan sanda, CP Sule Maku, ya fitar da jawabi ga manema labarai inda ya sanar da cewa bincike ya kankama tun tuni a kan harin.

Jawabin ya ce:

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Ebonyi, CP Philip Sule Maku, ya yi tir da harin da aka kai wa Makiyaya Fulani a rugarsu da ke dajin Ukwuachi a karamar hukumar Ebonyi.”

“A sakamakon harin an kashe mutane (2), wani Adamu Ibrahim, namiji mai shekaru 7 da kuma Jubril Ibrahim, namiji, ‘dan shekara 15 da haihuwa.” inji CP.

“An yi wa mutane (2) mummunan rauni wadanda yanzu haka su na jinya a babban asibitin koyar da aikin lafiya na gwamnati tarayya da ke Abakalili.”

A jiya kun ji cewa kudin da ake samu daga rijiyar mai ya haddasa rigima tsakanin gwamnatin jihar Bayelsa da ta Ribas duk da hukuncin da kotu ta yi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel