Babbar magana: Yadda shugabannin ƙanana hukumomi biyu suka ba hammata iska

Babbar magana: Yadda shugabannin ƙanana hukumomi biyu suka ba hammata iska

- Shugaban karamar hukumar Suleja , Alhaji Abdullahi Maji, da na karamar hukumar Gurara, Mista Yussuf Wali Gwamna sun sha dambe a wani taro

- Rikici ya kaure tsakaninsu ne kan wanda zai jagoranci kungiyar shugabannin kananan hukumomi na jihar Neja

- Lamarin ya kai ga har Wali Gwamna ya sumar da Maji tare da ji masa raunuka

Rahotanni sun kawo cewa rigima ta kaure a tsakanin Shugaban karamar hukumar Suleja , Alhaji Abdullahi Maji, da na karamar hukumar Gurara, Mista Yussuf Wali Gwamna, kan shugabancin kungiyar shugabannin kananan hukumomi na jihar Niger.

Wannan labari har ya kai su ga ba hammata iska a bainar taro, jaridar Leadership ta ruwaito.

An tattaro cewa dukkaninsu su biyu sun nuna ra’ayinsu na neman kujerar shugabancin kungiyar, sannan kowannensu ya ki hakura ya janye wa dan uwansa takarar.

Rahoton ya nuna cewa ana cikin haka ne, sai Wali Gwamna na karamar hukumar Gurara ya lakada wa Maji mugun duka wanda har sai da ya kai ga ya suma, inda aka kwashe shi zuwa wani asibitin kudi don jinyan raunukan da ya samu.

KU KARANTA KUMA: Babbar magana: Mawakin Buhari, Malam Yala ya ajiye aikin muƙamin SA na kakakin majalisar Kaduna

Babbar magana: Yadda shugabannin ƙanana hukumomi biyu suka ba hammata iska
Babbar magana: Yadda shugabannin ƙanana hukumomi biyu suka ba hammata iska Hoto: @dailytrust
Asali: UGC

Majiyoyi a wajen taron na wanda aka gudanar a Kaduna, sun ce an fara samun matsala ne a lokacin da aka nemi wakilan Jihar Neja da su jagoranci tawagar jihar zuwa Zariya.

Za su Zariya ne domin yi wa Masarautar Zazzau ta’aziyyar rasuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris.

Toh a nan ne sai shugaban karamar hukumar ta Suleja ya gabatar da kansa a matsayin shigaban kungiyar daga Jihar.

Don haka sai Wali Gwamna wanda ya nuna fusatarsa a fili kan ikirarin Maji, ya musanta cewa shi (Maji) ne shugabansu.

A kokarin da yayi na nuna bacin ransa ne bayan da tawagar ta wuce zuwa Zariya, shine ya kai sa ga lakada wa shugaban na karamar hukumar ta Suleja mugun duka.

Majiyoyin sun ce damben ya kai ga lalata dukkanin abin da ke kan saman teburin taron da kujeru sannan suka farfasa duk sauran kayayyakin.

KU KARANTA KUMA: Banda asarar dukiya: Ambaliyar ruwa ta halaka mutane 40 a Jigawa

An ce shugabannin biyu sun ja junansu ne zuwa tsakiyar dakin taron, inda suka fara dambe kafin sauran shugabannin kananan hukumomin da suke a wajen su shiga tsakani.

Mai ba gwamnan jihar Niger shawara a kan harkokin siyasa, Alhaji Nma Kolo, ya tabbatar da afkuwar lamarin. Ya ce gwamnatin jihar na bincike a cikin lamarin.

Kolo ya kuma bayyana cewa, shugabannin biyu sun kunyata jiharsu..

A wani labari na daban, mun ji cewa wasu fusatattun matasa a ranar Talata sun kai wa hadimin gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar da wasu jami'an gwamnatin jihar hari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel