Babbar magana: Mawakin Buhari, Malam Yala ya ajiye aikin muƙamin SA na kakakin majalisar Kaduna

Babbar magana: Mawakin Buhari, Malam Yala ya ajiye aikin muƙamin SA na kakakin majalisar Kaduna

- Mawakin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Yala ya ajiye mukaminsa a matsayin mai bayar da shawara ga kakakin majalisar Kaduna

- Malam Yala ya yi murabus ne a jiya Litinin, 28 ga watan Satumba

- Sai dai ya bayyana cewa dalili nasa na kansa ne ya sanya shi ajiye mukamin

Mawakin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya zama dan siyasa, wanda ya yi shahararriyar wakar nan ‘Yau Nigeria riko sai mai gaskiya’, Malam Ibrahim Sale Yala, ya yi murabus daga mukaminsa.

Malam Yala ya kasance mai bayar da shawara na musamman ga kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Ibrahim Zailani.

Ya bayyana cewa ba wani abune ya sanya shi ajiye mukamin ba illa wani dalili nasa na kansa

KU KARANTA KUMA: Allahu Akbar: Baturen ilimi na birnin tarayya Abuja, Marafa ya rasu

Babbar magana: Mawakin Buhari, Malam Yala ya ajiye aikin muƙamin SA na kakakin majalisar Kaduna
Babbar magana: Mawakin Buhari, Malam Yala ya ajiye aikin muƙamin SA na kakakin majalisar Kaduna Hoto: real_ibrahim_yala
Asali: Instagram

Mawakin ya wallafa hakan ne a shafinsa na Instagram, inda ya rubuta:

"Na yi murabus daga mukamina na mai bayar da shawara na musamman ga kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Hon. Yusuf Ibrahim Zailani, a jiya 28/9/2020. Ina son amfani da wannan kafar don yin godiya ga kakakin maalisar a kan damar da ya bani na yin aiki a karkashinsa.”

Ibrahim Yala ya zama sananne ne a lokacin kamfen din Shugaban kasa Buhari tun na 2003.

Mawakin, wanda ya kuma kasance jigo a jam’iyyar APC a Kaduna, ya fito a wasu fina-finan Kannywood irin su Gidan Badamasi.

KU KARANTA KUMA: Nufin Allah: Dattijuwa ta zama cikakkiyar likita tana da shekaru 50 (Hotuna)

Ya kasance Darakta Janar na labarai ga kungiyar kamfen din Sanata Uba Sani a lokacin zaben 2019, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A wani labari na daban, Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya bayyana cewa ya shirya sauka daga kujerar shugabanci idan Rotimi Amaechi, ministan sufuri ya ambaci gudunmawarsa ga jihar a matsayinsa na wanda ke rike da mukamin minista.

A cewar jaridar The Cable, Wike ya yi furucin ne a ranar Litinin, 28 ga watan Satumba, a lokacin wata hira a tashar AIT.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel