Da duminsa: Majalisar Dattijai ta dawo bakin aiki bayan hutun makonni takwas

Da duminsa: Majalisar Dattijai ta dawo bakin aiki bayan hutun makonni takwas

- Majalisar dattawa ta dawo zamanta a yau Talata, 29 ga watan Satumba, bayan hutun sama da watanni biyu

- Bayan bude taro da addu’a wanda Shugaban majjalisar dattawa, Ahmad Lawan yayi, ya bayyana cewa zai karonto wasikar da Buhari ya aiko kan dokar man fetur a zauren

- Har ila yau akwai muhimman batutuwa da dama da yan majalisar za su zanta a kai

Majalisar dattawan Najeriya ta dawo zama bayan hutun shekara da ta tafi na tsawon fiye da watanni biyu.

Bayan nan, sai yan majalisar dokokin na tarayya suka shiga wani taro na sirri.

Majalisar dattawan ta dakatar da zamanta a ranar 23 ga watan Yuli, sannan ta saka ranar dawowa a kan 15 ga watan Satumba, amma sai mukaddashin magatakardar majalisar ya sanar da dage dawowar zuwa ranar 29 ga watan Satumba.

KU KARANTA KUMA: Ku sani: Dalilin da ya sa gwamnatin Kano ta kama jarumin Kannywood, Naburaska

Da duminsa: Majalisar Dattijai ta dawo bakin aiki bayan hutun makonni takwas
Da duminsa: Majalisar Dattijai ta dawo bakin aiki bayan hutun makonni takwas Hoto: @DrAhmadLawan
Asali: Twitter

An fara ganawar sirrin da misalin karfe 10:41 na safe bayan Shugaban majalisar dattawan, Ahmad Lawan, ya jagoranci addu’o’i sannan ya amince da kuri’u da tsare-tsaren ranar.

An tsara muhimman abubuwa da dama wanda yan majalisar za su yi nazari a kansu.

Daya daga cikin wadannan abubuwa shine dokar man fetur wanda Mista Lawan ya sanar da cewa za a karanta wata wasika daga Shugaban kasa Muhammadu Buhari game da hakan a zauren majalisar, a yau Talata.

Wani batu da za a zanta a kai shine rahoton kwamitin kasafin kudin da za a kashe na 2021-2023, jaridar Premium Times ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Zan sauka daga Gwamna idan Amaechi ya nuna aiki ɗaya da yayi wa Rivers - Wike

Taron majalisar na kan gudana a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

A gefe guda, mun ji cewa Ministar bada tallafi da agaji da cigaban al’umma, Hajiya Sadiya Umar-Faruk, ta kaddamar da shirin CCT na gwamnatin tarayya a jihar Bayelsa.

Sadiya Umar-Faruk ta ce gwamnati za ta rika biyan marasa hali N5000 duk wata a Bayelsa.

Gwamnatin tarayya ta kan zabi Bayin Allah da su ka fi kowa jikkata domin ta taimaka masu da abin da za su rike rayuwarsu a tsarin nan na CCT.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel