Goodluck Jonathan ya yi wa Shugaba Buhari bayanin halin da ake ciki a Mali

Goodluck Jonathan ya yi wa Shugaba Buhari bayanin halin da ake ciki a Mali

- Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da Dr. Goodluck Jonathan a Aso Villa

- Buhari ya tattauna da Goodluck Jonathan a matsayinsa na jakadan ECOWAS

- Jonathan da Magajinsa su na ta kokarin ganin an samu zaman lafiya a Mali

Shugabannin kasashen yammacin Afrika da kungiyar ECOWAS, su na shirin sake yin wani zama domin tattauna halin da ake ciki a kasar Mali.

An sanar da wannan mataki ne bayan zaman da aka yi tsakanin mai girma Muhammadu Buhari da tsohon shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan.

Rahotanni sun tabbatar da cea Dr. Goodluck Jonathan ya kai ziyara zuwa fadar shugaban kasa ne a jiya ranar Litinin, 28 ga watan Satumba, 2020.

KU KARANTA: Buhari da Jonathan sun hadu a Abuja

Mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya yi karin haske game da yadda tattaunawar Jonathan da Mai gidansa ta kasance.

Sabon shugaban ECOWAS, Nana Akufo-Addo na Ghana ne ya bukaci ayi zama na musamman.

Jonathan ya shaidawa Buhari cewa har yanzu sojojin tawayen Mali ba su cika sharudan da ECOWAS ta ba su na mikawa farar hula mulki ba.

Jawabin da hadimin shugaban kasar ya fitar ya bayyana cewa sojoji su na cigaba da rike kujerar mataimakin shugaban kasa, akasin sharadin da aka sa.

KU KARANTA: 2023: Wasu ‘Yan Arewa su na son Jonathan ya koma mulki

Goodluck Jonathan ya yi wa Shugaba Buhari bayanin halin da ake ciki a Mali
Goodluck Jonathan da Shugaba Buhari Hoto: Sun
Asali: UGC

Haka zalika ba a gama tabbatar da aikin da mataimakin shugaban kasa zai yi a gwamnatin Mali ba.

Adesina ya ce: “Shugaba Buhari ya bukaci jakadan ECOWAS na musamman (Jonathan), ya gabatar da rahoto ga sabon shugaban ECOWAS, wanda zai sanar da mu game da matakin da za a dauka."

Idan za ku tuna sojoji sun kafa gwamnatin rikon kwarya a Mali bayan hambarar da shugabannin kasar a wani juyin-mulki da aka yi watan da ya wuce.

Dr. Goodluck Jonathan shi ne Jakada na musamman da ECOWAS ta tura zuwa kasar Mali.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel