Fitattun sarakunan arewa 7 da rasuwarsu ya girgiza mutanen Najeriya a 2020

Fitattun sarakunan arewa 7 da rasuwarsu ya girgiza mutanen Najeriya a 2020

- An yi rashin sarakuna masu yawa a sassa daban-daban na Najeriya musamman ma arewacin kasar a shekarar 2020

- Mutuwar sarki babban rashi ne ga al'umma kuma abu ne da ke girgiza mutane duba da irin muhimmiyar rawar da suke taka wa

- Wasu daga cikin sarakunan da Allah ya yiwa rasuwa a wannan shekarar suna hada da Sarkin Rano, Sarkon Biu, Sarkin Zazzau da Sarkin Kauran Namoda

Mutuwar basarake da al'umma ke kauna lamari ne da ke girgiza al'umma a duk lokacin da hakan ya faru sannan akwai bukatar a maye gurbinsa da wani sarkin.

Tun farkon wannan shekarar, Allah ya yi wa manyan sarakuna da dama rasuwa a Najeriya. A wannan rahoton mun tattaro muku wasu daga cikinsu kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Fitattun sarakunan arewa 7 da rasuwarsu ya girgiza 'yan Najeriya a 2020
Fitattun sarakunan arewa 7 da rasuwarsu ya girgiza 'yan Najeriya a 2020. Hoto daga @PremiumTimes/@MobilePunch
Asali: Twitter

1. Alhaji Ahmad Muhammad Asha - Sarkin Kauran Namoda

A watan Mayun 2020 ne Allah ya yi wa Alhaji Ahmad Muhammad Asha, Sarkin Kiyawan Kaura na Namoda rasuwa a jihar Zamfara. Ya rasu yana da shekaru 71.

Ya yi aiki a matsayin direktan kudi da ma'aji a kananan hukumomi masu yawa ciki har da Kaura Namoda, Gusau da Maru kafin nada shi sarki a 2004.

Ya dade yana fama da ciwon suga da hawan jini. Ya rasu ya bar mata uku da yara 11 cikinsu har da Alh. Sanusi Muhammad Asha da ya gaje shi.

2. Alhaji Shehu Idris - Sarkin Zazzau

Allah ya yi wa sarkin Zazzau, Shehu Idris rasuwa a ranar Lahadi 20 ga watan Satumban 2020. Ya rasu ne a asibitin sojoji na 44 da ke Kaduna yana da shekaru 84 a duniya.

A lokacin rayuwarsa, Sarkin ya yi zamani da gwamnoni na farar hula da soji 20, cikinsu har da Gwamna Nasir El-Rufai mai ci a yanzu.

Mutane da dama sunyi ta fadin abin alheri da sarkin ya aikata lokacin rayuwarsa ciki har da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da ya ce sarkin ne ya taimaka masa yin sulhu yayin da ake rikici a Plateau.

Kawo yanzu dai ba a nada sabon sarki da zai maye gurbinsa ba duk da rahotanni sun ce masu zaben sarki sun mika sunayen mutane uku ga gwamnan jihar don ya zaba sabon sarki.

DUBA WANNAN: Mayakan ISWAP sun afka wa tawagar ma'aikatan gwamnatin jihar Borno

3. Micheal Ameh Oboni II - Atah na Igala

Basaraken na jihar Kogi ya rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa a babban birnin tarayya Abuja a watan Agusta bayan shekaru bakwai kan sarauta.

Kawo yanzu masarautar ba ta nada sabon sarki da zai maye gurbinsa ba.

4. Tafida Abubakar Ila II - Sarkin Rano

Allah ya yi wa sarkin Rano, Dakta Tafida Abubakar Ila II rasuwa a ranar 2 ga watan Mayun 2020 a asibitin kwararru ta Nasarawa, Kano yana da shekaru 74 a duniya.

Sarkin ya rasu ya bar mata biyu da yara 17. Yana daya daga cikin sabbin sarakun hudu da Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya nada.

An nada shi sarki ne a ranar 9 ga watan Mayun shekarar 2019 tare da wasu sarakuna uku a jihar.

5. Kyari Ibn Umar Elkanemi - Shehun Bama

Allah ya yi wa Kyari Ibn Umar Elkanemi rasuwa a ranar 27 ga watan Afrilun 2020.

Rahotanni sun ce marigayin ya taka muhimmiyar rawa wurin tabbatar da zaman lafiya da hadin kai tsakanin masu sarauta musamman lokacin da aka raba masarautar Dikwa zuwa gida biyu a 2010 zuwa Dikwa da Bama.

Marigayin ya yi aiki tare da hakimai da dagatai da masu unguwanni don ganin martabar da masu sarauta ke da shi bai zube ba.

Gwamna Babagana Zulum ya nada magajinsa Mohammed Musa jim kadan bayan rasuwarsa.

KU KARANTA: Hotuna: Obaseki ya kai wa Buhari ziyara bayan kayar da dan takarar APC a zabe

6. Alhaji Umar Mustapha Aliyu - Sarkin Biu

Duk dai a jihar Borno, Sarkin Biu, Alhaji Umar Mustapha Aliyu ya rasu a ranar 15 ga watan Satumban 2020 bayan shafe shekaru 31 kan kujerar sarauta.

Ya rasu yana da shekaru 80 a duniya. A zamaninsa ya kirkiri karin masarautu da suka hada da Shafa, Gunda, Kwaya-Bura, Sabon Kasuwa da Buratai.

An maye gurbinsa da babban dansa, Alhaji Mustapha Umar Mustapha da ke rike da saurautan Maidala kafin rasuwar Sarkin.

7. Honest Stephen Irmiya - Sarkin Bachama

Honest Irmiya Stephen ne sarki na 28 a masarautar Bachama da ta kunshi garuruwa a kananan hukumomin Numan da Lamurde a jihar Adamawa.

Ya rasu a ranar 27 ga watan Yunin 2020 yana da shekaru 66 a duniya. Ya bar ayyuka da dama da al'umma ke tuna shi da su.

Ya yi murabusa daga aikin soja a 2012 a lokacin da aka zabe shi don maye gurbin Homun Asaph Zadok. Ya fito daga gidan sarauta ta Nomupo.

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya lashe kyautar Zik a rukunin shugabanci na shekarar 2019 kamar yadda Farfesa Pat Utomi ya sanar a ranar Alhamis.

Zulum wanda shine mutum na takwas cikin jerin wadanda suka lashe kyautar an karrama shi ne saboda shugabanci na gari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel