Gwamna Mohammed ya sallami shugaban ma'aikatan jihar Bauchi daga aiki

Gwamna Mohammed ya sallami shugaban ma'aikatan jihar Bauchi daga aiki

- Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya kori shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar, Ahmed Ma'aji daga aiki

- Gwamnan ya kuma maye gurbinsa da Dakta Bala Lukshi a matsayin shugaban ma'aikatan jihar na riko

- Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ta fito daga bakin Direktan Watsa Labarai na gwamnatin jihar Bauchi, Suleiman Dambam

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ya sallami Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Ahmed Ma'aji kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Kazalika, gwamnan ya nada Dakta Bala Lukshi a matsayin shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar na rikon kwarya.

Hakan na cikin wata sanarwa ce mai dauke da sa hannun Direktan Watsa Labarai na gwamnatin jihar Bauchi, Suleiman Dambam da ya raba wa manema labarai a daren ranar Juma'a.

DUBA WANNAN: APC ta dakatar da hadimin Buhari, surukin Tinubu da wasu mutane takwas

Gwamna Mohammed ya sallami shugaban ma'aikatan jihar Bauchi daga aiki
Gwamna Mohammed ya sallami shugaban ma'aikatan jihar Bauchi daga aiki. Hoto daga MobilePunch
Asali: Twitter

Dambam ya ce nadin Lukshi zai fara aiki ne daga ranar Juma'a 25 ga watan Satumba.

Ya ce kafin nadinsa, Dakta Bala Lukshi ne sakataren dindindin mafi girma a ma'aikatun jihar ta Bauchi.

KU KARANTA: Hotuna: Obaseki ya kai wa Buhari ziyara bayan kayar da dan takarar APC a zabe

Wani sashi na wasikar ya ce, "Na rubuta wannan wasikar don sanar da kai nadin da na maka a matsayin shugaban riko na ma'aikatan gwamnatin jihar Bauchi da zai fara aiki daga ranar 25 ga watan Satumban 2020.

"An nada ka shugaban riko ne a lokacin da wannan gwamnatin ma ci yanzu ke kokarin farfado da inganta ayyukan ma'aikatan gwamnati a jihar."

Gwamnan ya shaida wa sabon shugaban rikon cewa yana sa ran ba zai gaza ba wurin kwazo da kishin jihar wurin gudanar da ayyukansa.

Har wa yau, ya taya shi murna tare da shawartarsa ya yi amfani da kwarewarsa da gogewarsa wurin cimma nasara a ayyukansa.

A wani labarin, gwamnan Borno, Babagana Zulum ya lashe kyautar Zik a rukunin shugabanci na shekarar 2019 kamar yadda Farfesa Pat Utomi ya sanar a ranar Alhamis.

Zulum wanda shine mutum na takwas cikin jerin wadanda suka lashe kyautar an karrama shi ne saboda shugabanci na gari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel