Yadda bai wa PDP damar lallasa APC a zaben Edo - Buhari ya yi bayani

Yadda bai wa PDP damar lallasa APC a zaben Edo - Buhari ya yi bayani

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake jaddada cewa shine shugaba a tafiyar jam'iyyar APC

- Buhari ya ce,a matsayinsa na shugaba, ya dauka alhakin lallasa jam'iyyar APC da aka yi a zaben jihar Edo

- Shugaban kasar ya bayyana cewa shine shugaban Najeriya kuma dole ya tabbatar da cewa an bi abinda jama'a ke so

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma'a, 25 ga watan Satumba, ya ce ya dauka alhakin lallasa APC da aka yi a zaben ranar Asabar da ta gabata na gwamnoni.

Shugaban kasar ya sanar da hakan a gidan gwamnati bayan karbar sabon gwamna jihar Edo, Godwin Obaseki, tare da mataimakinsa Philip Shaibu da wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP.

Buhari ya ce a matsayinsa na babban jiigo a jam'iyyarsa, shine yakamata a dora wa laifin komai ballantan a lokacin da aka lallasa su a zabe.

Shugaban kasar ya jaddada cewa, duk da yana da jam'iyya, amma ya zama dole garesa da ya tabbatar da an bi ra'ayin jama'a yayin zaben shugaba.

Shugaba Buhari ya ce: "Mun rasa jihohi masu yawa a fadin kasar nan. A saboda haka bana son gujewa wani hakki da ya hau kaina. Ni ne shugaban jam'iyyata a kasar nan.

"Ina kokarin tabbatar da cewa an gina jam'iyyar da wayewa ta zamai, bin dokoki da kuma mutunta hakkokin jama'a"

KU KARANTA: Dauke da tsohon ciki matar aure tayi kundunbala ta fada cikin ruwa domin ceto mijinta da kifi ke shirin cinyewa

Yadda na sa PDP ta lallasa APC a zaben Edo - Buhari ya yi bayani
Yadda na sa PDP ta lallasa APC a zaben Edo - Buhari ya yi bayani. Hoto daga @Nigeriagov
Asali: Twitter

KU KARANTA: Borno: An rasa rayuka 3 a sabon harin 'yan ta'addan Boko Haram

A wani labari na daban, Lai Mohammed, ministan yada labarai da al'adu, ya ce mulkin kasar nan karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari, na kokarin saka kasar nan a hanyar da ta dace.

A yayin jawabi ga manema labarai a ranar Alhamis domin bayyana shirye-shiryen shagalin bikin cikar Najeriya shekaru 60, Mohammed ya ce tun bayan samun 'yancin kasar, an fuskanci yakin basasa, rikicin siyasa da kuma rashin tsaro.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel