Sabon Sarki zai fito ne daga Nahiyar Asiya inji Sanata Shehu Sani

Sabon Sarki zai fito ne daga Nahiyar Asiya inji Sanata Shehu Sani

- Sanata Shehu Sani ya yi hasashe game da nadin sabon Sarki a Zazzau

- ‘Dan siyasar ya nuna inda magajin Marigayi Sarki Shehu Idris zai fito

- A cewarsa za a dauko sabon Sarkin da za a nada ne daga Nahiyar Asiya

Kwamred Shehu Sani ya tofa albarkacin bakinsa game da wanda ake sa ran cewa zai zama sabon Sarkin Zazzau.

Shahararren ‘dan siyasar ya yi wani magana a kaikaice a shafinsa na Facebook, yayin da ake jiran sanarwar sabon sarki.

Shehu Sani wanda ya saba tsoma bakinsa a lamuran yau da kullum a Najeriya, ya yi wata gajerar magana a Facebook.

Tsohon Sanatan bai kama sunan wanda zai zama sarkin Zazzau ba, amma ya bada satar amsa da ta nuna inda ya dosa.

KU KARANTA: Hasken Fadar Kano ya na goyon bayan Mallawa su yi mulkin Zazzau

Kwamred Sani ya rubuta cewa sabon Sarkin da za a nada zai fito ne daga Nahiyar Asiya.

Sani ya bayyana wannan ne a shafin sada zumuntansa Facebook a ranar Laraba, 23 ga watan Satumba, 2020.

Daga lokacin da Sani ya yi wannan jawabi da kimanin karfe 6:00 na yamma zuwa yanzu, an yi ta samun martani.

Tsohon ‘dan majalisar bai yi wani karin bayani ba face wannan gajerar magana da ya yi.

Sabon Sarki zai fito ne daga Nahiyar Asiya inji Sanata Shehu Sani
A makon nan Ahmad Bamalli ya shigo Najeriya Hoto: The Big Chill
Asali: UGC

KU KARANTA: Mai dakin El-Rufai ta na so Mace ta yi mulkin Zazzau

Amma masana da sauran masu fashin baki su na ganin cewa Ahmad Nuhu Bamalli ne wanda Shehu Sani ya ke nufi.

Dalili kuwa shi ne Ahmad Nuhu Bamalli ya kasance Jakadan Najeriya a kasar Thailand da ke Kudancin Asiya.

Idan za ku tuna sauran manyan masu neman sarautar Zazzau su ne: Iyan Zazzau, Yariman Zazzau, Turakin Zazzau.

Daga cikin wadannan sarakai da aka ambata, babu wanda ya ke Asiya ko ma kasar waje sai Magajin Garin Zazzau.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel