Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC ta dakatad da gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi

Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC ta dakatad da gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi

- Sakamakon fadi a zaben jihar Edo, jam'iyyar APC ta dakatad da shugaban gwamnonin Najeriya

- Jam'iyyar ta zargeshi da laifin yi mata zagon kasa ta hanyar taimakawa abokin adawa

- Jam'iyyar APC ta sha kashi a zaben gwamnan jihar Edo ranar Asabar, 19 ga Satumba

Majalisar zartarwan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Ekiti ta dakatad da gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi.

Rikicin cikin gidan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Ekiti ta dau sabon salo ranar Juma'a.

A cewar jam'iyyar, an dakatad da gwamnan ne sakamakon irin yankar bayan da ya ke yiwa jam'iyyar musamman rawan da ya taka a zaben gwamnan jihar Edo da aka kammala, ChannelsTV ta samu labari.

A cikin jerin tuhume-tuhumen da suka yiwa Fayemi, mambobin majalisar zartarwa ya taimakawa gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, na People’s Democratic Party(PDP) wajen kayar da Fasto Ize-Iyamu na jam'iyyar APC.

Hakazalika, mambobin majalisar sun sanyawa shugaban jam'iyyar, Paul Omotosho, takunkumi saboda dakatad da su da yayi.

Wadanda suka rattafa hannu kan takardan sune: Sanata Tony Adeniyi, Sanata Babafemi Ojudu, Sanata Dayo Adeyeye, tsohon dan majalisa, Bimbo Daramola, Robinson Ajibiye, Oyetunji Ojo, Adewale Omirin da Femi Adeleye.

Wannan dakatarwan na zuwa ne sa'o'i 24 bayan dakatad da hadimin Buhari, Sanata Babafemi Ojudu, da wasu mutane 10.

KU KARANTA: Ba zamu fasa zuwa yajin aiki - Kungiyar kwadago ta bayyanawa gwamnatin tarayya

Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC ta dakatad da gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi
Credit: ChannelsTV
Asali: Twitter

DUBA NAN: Haramta Biza ga masu magudi: Mu ke da hakkin zaban wadanda zasu shiga kasarmu - Ingila ta yiwa Najeriya raddi

A wani labarin daban, Kungiyoyin kwadago a Najeriya NLC da TUC, a ranar Alhamis, sun yi watsi da hukunicn kotun ma'aikata da ta haramta musu zuwa yajin aikin da za'a fara ranar Litinin.

NLC da TUC sun bayyana hakan ne bayan baran-baran a ganawar da akayi tsakaninsu da gwamnatin tarayya a daren Alhamis.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel