Za mu kafa kasar Yarabawa ba tare da tada fitina ba - Farfesa Akintoye

Za mu kafa kasar Yarabawa ba tare da tada fitina ba - Farfesa Akintoye

- Wasu ƙungiyoyin Yarabawa sun yunƙuro suna son ɓallewa daga Najeriya su kafa kasa daban ta su ta Yarabawa

- Shugaban gamayyar ƙungiyoyin a ƙarƙashin YWC, Farfesa Banji Akintoye ya ce ba za su zubar da jini ba wurin neman kafa ƙasar

- Farfesa Akintoye ya ce sun fara da ƙungiyoyi 45 amma a yanzu suna da ƙungiyoyi 107 a ƙarƙashin su

Za mu kafa kasar Yarabawa ba tare da tada fitina ba - Farfesa Akintoye
Za mu kafa kasar Yarabawa ba tare da tada fitina ba - Farfesa Akintoye. Hoto daga @SaharaReporters
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Borno: An sun kashe manyan kwamandojin 'yan Boko Haram 7 a Tafkin Chadi

Shugaban Kungiyar Yarabawa ta Yoruba World Congress, Farfesa Banji Akintoye ya ce ƙungiyar za ta kafa ƙasar Yarabawa ta tare da zub da jini ba.

Ya yi wannan jawabin ne a ranar Laraba yayin bikin tunawa da Yaƙin Kirji kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Ya ce ƙungiyar ta na da ƙungiyoyi 107 a ƙarƙashin ta da ke na niyyar ganin kafuwar ƙasar Yarabawa kamar yadda The Punch ta ruwaito.

KU KARANTA: Dalilin da yasa 'yan Najeriya ke korafi kan karin kudin wutar lantarki - Sanusi II

Ya ce, "Mun daɗe muna cewa za mu kafa ƙasar Yarabawa. Yoruba World Congress ta duƙufa don ganin yarabawa sun samu matsayin da ya dace da su a tsakanin ƙasashe.

"Da muka fara wannan tafiyar, mun fara ne da ƙungiyoyi 45 amma yanzu muna da kungiyoyi 107 mabanbanta a ƙarƙashin mu.

"Su kan ce ni ba bane mai karaya a kan abinda na sa a gaba; Ba kowane lokaci na ke hakan ba. Amma idan har mun amince a kan abu, ban iya cin amana ba.

"Za mu kafa ƙasar Yarabawa ba tare da zubar da jini ba; ba za mu karya dokokin Najeriya ba. Idan akwai wasu da ke son tayar da hankali, za mu fada musu su dena."

A wan labarin daban, Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna, NAFDAC, ta rufe kamfanonin kera magungunan dabobi na jabu a karamar hukumar Bichi na jihar Kano.

Shugaban hukumar na jihar, Shaba Muhammad ne ya bayyana hakan yayin wata sumame da jami'an hukumar suka kai Laraba a Bichi kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel