Mawakin Kano da aka yanke wa hukuncin kisa zai iya zuwa har kotun koli - Ganduje

Mawakin Kano da aka yanke wa hukuncin kisa zai iya zuwa har kotun koli - Ganduje

- Gwamnatin jihar Kano ta ce mawakin da aka yanke wa hukuncin kisa mai suna Yahaya Sharif-Aminu, yana da damar daukaka kara zuwa kotun koli.

- Gwamnan Abdullahi Ganduje ya fadi hakan yayin zantawa da manema labaran gidan gwamnati a Abuja bayan taro da Shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Kotun Musulunci ta yanke wa AMinu Shariff hukunci kisa ta hanyar rataya bayan batanci da yayi ga Annabi

Kotun shari'ar Musulunci ta jihar kano ta yanke wa Shariff-Aminu dan shekara 22 hukuncin kisa bayan an kama shi dumu-dumu da laifin batanci ga manzon Allah, a wata wakarsa da ta yi ta yawo a kafar sada zumuntar zamani ta WhatsApp.

Alkali Aliyu Muhammad Kani yace wanda ake zargin zai iya daukaka kara matukar bai gamus da hukunci da aka yanke masa ba.

"Ya riga ya daukaka kara," a cewar Ganduje a ranar Talata.

"Za'a cigaba da shari'a har kotun koli," inji Ganduje.

A halin yanzu muna jiran hukunci ne kawai.

Dangane da batun da Ganduje ya yi ma Buhari Godiya akan harkokin tsaro da kuma taimakon da ya bai wa Kano lokacin da cutar Coronavirus ta barke.

KU KARANTA: Tsohuwa 'yar shekara 57 da ta kammala JS3 na sakandare tace tana so ta zama ma'aikaciyar lafiya

Mawakin Kano da aka yanke wa hukuncin kisa zai iya zuwa har kotun koli - Ganduje
Mawakin Kano da aka yanke wa hukuncin kisa zai iya zuwa har kotun koli - Ganduje. Hoto daga Premium Times
Asali: UGC

KU KARANTA: Sanata Ali Ndume ya koka akan kisan Kanal din soja da 'yan Boko Haram suka yi a Borno

A wani labari na daban, kungiyar Malaman jihar Kano da kungiyoyin sakai na (NGO) na jihar Kano sun nuna goyon bayansu dari bisa dari akan hukuncin kisan da aka yankewa mawakin da yayi batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).

Wannan ya fito ne ta wata sanarwa da shugaban kungiyar hadin guiwar, Farfesa Musa Muhammad Borodo, wanda yace kama mawakin da kuma hukuncin da aka yanke masa shine ya kawo karshen wannan lamari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel