Ku daina karban bashi don ayyuka - Muhammadu Sanusi II ga gwamnati

Ku daina karban bashi don ayyuka - Muhammadu Sanusi II ga gwamnati

- Tsohon gwamnan CBN kuma tsohon sarkin Kano ya baiwa gwamnatin shugaba Buhari shawara

- Sanusi ya dawo Najeriya daga Ingila domin ta'aziyyar rasuwar Sarkin Zazzau

- Ya bukaci Najeriya ta samar wani hanyar samun kudin shiga sabanin man fetur

Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, ya shawarci gwamnatoci su daina karban bashi domin aiwatar da ayyuka.

Hakazalika ya bayyana cewa rashin neman wani hanyar kudin shiga sabanin man fetur tsawon shekaru 60 yanzu ya haifar da halin talaucin da ake ciki yau.

Tsohon gwamnan bankin CBN ya ce maimakon karban bashi, kamata yayi gwamnatoci su zuba kudi wajen gina mutane da kuma manufar janyo hankalin masu sanya hannun jari.

Ya bada wannan shawara ne a taron sanya hannun jarin da gwamnatin jihar Kaduna ta shirya ranar Talata, The PUNCH ta ruwaito.

Sanusi yace: "Yayinda kowa ke zuwa wajen gwamnatin tarayya neman mafita, gaskiyar magana itace gwamnatin tarayya bata wani rawan takawa a tattalin arzikin kasa."

Tsohon Sarkin ya tunatarwa da jama'a yadda tattalin arzikin Najeriya ya kasance kafin samuwar arzikin man fetur.

DUBA NAN: Sarautar Zazzau: Tsakanin na kusa da Buhari, da abokin El-Rufa'i

Ya bayyana cewa gabanin samuwar man fetur, an gina tattalin arzikin Najeriya ne kan yadda ba zata girgiza ba idan an samu matsala a kasuwar duniya.

A kan dauke hankali daga arzikin mai, ya kwatanta Najeriya da kasar Malaysiya, wacce ta cigaba daga fitar da kananan kayayyaki zuwa kere-keren abubuwansu cikin shekaru 30 daga 1970 zuwa 200.

Ku daina karban bashi don ayyuka - Muhammadu Sanusi II ga gwamnati
Ku daina karban bashi don ayyuka - Muhammadu Sanusi II ga gwamnati
Asali: Twitter

A bangare guda, rahotanni daga gidan sarautar Zazzau da gidan gwamnatin jihar na nuna cewa cikin mutane biyu za'a zabi sabon sarki; daya na kusa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari da kuma abokin gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i.

Na farko, Alhaji Munir Ja'afari, mai shekaru 66, babban dan kasuwa kuma tsohon shugaban hukumar NIMASA, sannan Alhaji Ja'afaru Nuhu Bamalli, tsohon jakadan Najeriya zuwa kasar Thailand.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel