Annobar COVID-19: Karin bayani ga masu neman tallafin tsarin MSME a yanar gizo

Annobar COVID-19: Karin bayani ga masu neman tallafin tsarin MSME a yanar gizo

- Gwamnatin Tarayya ta shigo da tsarin MSME na taimakawa ‘yan kasuwa

- Za a tallafawa wadanda annobar COVID-19 ta durkusar da hanyar cin su

- A ranar 15 ga watan Oktoba, 2020 za a rufe rajistar neman wannan tallafi

A ranar Litinin dinnan ne gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bude shafin da za a bada jari ga kananan da matsakaitan ‘yan kasuwa.

Gwamnatin tarayya ta shigo da wannan tsari ne domin a tallafawa ‘yan kasuwan da annobar cutar Coronavirus ta gurgunta a fadin Najeriya.

Ana sa ran cewa Najeriya za ta batar da Naira tiriliyan 2.3 domin a fita daga kangin COVID-19, saboda gudun tattalin arzikin kasar ya durkushe.

Akalla kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa mutum miliyan 1.7 za su amfana da wannan tsari gwamnati ta shigo da shi domin bunkasa tattali.

Jaridar Daily Trust ta yi bayani game da yadda za a yi a samu wannan jari:

1. Mai bukatar jari zai shiga shafin yanar gizo na https://www.survivalfund.ng ko kuma http://www.survivalfundapplication.com.

2. Idan mutum ya shiga wannan shafi sai ya nemi inda ake yin rajista domin neman rukunin tallafin da zai shiga.

KU KARANTA: Layin mai za su dawo saboda sabon yajin aikin NARTO

Rukunin wadanda ake ba tallafi

• Sahun farko na wadanda ake ba tallafi a tsarin MSME su ne ‘yan kasuwan da su ka gaza biyan ma’aikatansu a watanni uku da su ka wuce.

Gudumuwar tallafin albashin da za a bada a nan ya na tsakanin N30, 000 ne zuwa N50, 000.

• Sahu na biyu su ne masu ma’adanai da kamfanonin da su ke hada abubuwa.

• Sahu na uku su ne kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa.

3. Daga nan sai mutum ya zabi sahun da zai shiga

Sharuda da matakai

Masu neman tallafin nan za su bi daki-daki wajen rajista.

Ga abubuwan da ake bukata a rajista

• Rajistar bayanin mutum

A nan za a sa sunaye, adireshi, lambar salula, akwatin email, jinsi, ranar haihuwa, jiha da sauransu.

• Bude akawun

Za a turo da bayanan sirri a wayar salula da akwatin email.

• Rajistar kamfani ko kungiya

A nan kuma za a bukaci takardun CAC, da na SMEDAN da na harajin kamfani da kuma lambar asusun banki.

KU KARANTA: Biu ta samu sabon Sarki

• Kammala rajista

A nan ne za a bukaci sunayen ma’aikata 10 da hujjar biyan albashinsu.

Shi kenan sai a san ran samun wannan gudumuwa.

Lokacin rajista

Masu harkar makarantu za su fara rajista ne a ranar 21 ga Satumba.

Masu gidan abinci da wuraren kallo da shakatawa za su fara rajista a ranar 25 ga Satumba.

‘Yan kasuwa za su fara rajista a ranar 28 ga Satumba.

Za a rufe rajista a ranar 15 ga watan Oktoba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel