Shehu Idris ya zauna da Abba Kyari, Hameed Ali, Makarfi zuwa El-Rufai a mulki

Shehu Idris ya zauna da Abba Kyari, Hameed Ali, Makarfi zuwa El-Rufai a mulki

- Alhaji Shehu Idris ya rasu bayan shekaru 45 ya na kan gadon sarautar Zazzau

- A tsawon lokacin da ya yi ya na mulki, ya yi zamani da Gwamnoni 20 a Kaduna

- Alhaji Ahmad Makarfi ne wanda ya fi dadewa a cikin wadannan Gwamnonin

Kafin rasuwarsa, Marigayi Sarki Alhaji Shehu Idris ya yi shekaru 45 da tsawon watanni bakwai a kan karagar mulkin kasar Zazzau.

A wannan lokaci, Mai martaban ya yi zamani da gwamnoni 20 na farar hula da mulkin soji da aka yi a Kaduna tun daga 1975 zuwa 2020.

Ga jerin gwamnonin jihar Kaduna da Alhaji Shehu Idris ya zauna da su. An fara ne tun lokacin Kaduna ta na tsohuwar jihar Arewa.

1. Abba Kyari

Marigayi Birgediya Janar Abba Kyari shi ne gwamna a lokacin da Alhaji Shehu Idris ya zama Sarkin Zazzau, sun yi watanni 5 ne kacal tare.

2. Usman Jibrin

Kyaftin Usman Jibrin ya zauna da Shehu Idris na shekaru biyu a matsayin gwamna. Asalinsa mutumin Nasarawa ne wanda ya rasu a 2011.

3. Muktar Muhammed

Muktar Muhammed wani tsohon sojan sama ne da ya yi gwamna a tsohuwar jihar da aka sani da Arewa ta tsakiya tsakanin shekarar 1977 zuwa 1978.

Shehu Idris ya zauna da Abba Kyari, Hameed Ali, Makarfi zuwa El-Rufai a mulki
Mutane wajen jana'izar Sarkin Zazzau
Asali: Twitter

KU KARANTA: Wadanda ake yi wa harin kujerar Sarki bayan rasuwar Shehu Idris

4. Ibrahim Alfa

Ibrahim Mahmud Alfa shi ne sojan karshe da ya rike gwamna a Kaduna kafin ayi zaben 1979. Marigayin ya yi shekara daya tare da Sarki Shehu Idris.

5. Balarabe Musa

Alhaji Balarabe Musa shi ne gwamnan farar hula na farko da ya yi zamani da Shehu Idris. Tsohon gwamnan ya na cikin wadanda su ka ga rasuwar Sarki.

6. Abba Rimi

Abba Rimi ya yi gwamna bayan majalisar Kaduna ta tsige Mai girma Balarabe Musa a 1981.

7. Lawal Kaita

Alhaji Lawal Kaita ya na cikin sahun wadanda su ka zauna da Sarkin Zazzau Shehu Idris, Kaita bai dade da marigayin ba aka yi juyin mulki a 1983.

8. Usman Mu’azu

Usman Muazu ya yi mulki tsakanin 1984 zuwa 1985, a lokacin gwamnatin sojin Muhammadu Buhari.

Sauran gwamnonin su ne:

9. Dangiwa Umar

1985 – 1988

10. Abdullahi Sarki Mukhtar

1998 - 1990

11. Abubakar Tanko Ayuba

1990 – 1992

KU KARANTA: Buhari ya tada Tawaga zuwa jana'izar Sarkin Zazzau

12. Mohammed Dabo Lere

1992 – 1993

13. Lawal Jafaru Isa

1993 - 1996

14. Hameed Ali

1996 – 1998

15. Umar Faruk Ahmed

1998 - 1999

16. Ahmed Muhammad Makarfi

1999 – 2007

17. Namadi Sambo

2007 – 2010

18. Patrick Ibrahim Yakowa

2010 – 2012

19. Mukhtar Ramalan Yero

2012 – 2015

20. Nasir El-Rufai

2015 zuwa yau.

Dazu kun ji cewa a dalilin mutuwar Sarkin Zazzau, Shehu Idris, gwamnati ta ce babu aiki a Jihar Kaduna a ranar Laraba mai zuwa.

Wani hadimin Gwamna Nasir El-Rufai ya fitar da wannan sanarwa a ranar Lahadi da yamma.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel