Hotunan yadda dandazon jama'a suka cika wajen jana'izar Sarkin Zazzau

Hotunan yadda dandazon jama'a suka cika wajen jana'izar Sarkin Zazzau

- Gawar Marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ta isa birnin Zaria

- Tuni dai dandazon jama'a suka hallara domin jana'izar marigaayin wanda ake yi a yanzu haka

- Sarki Idris ya amsa kiran mahaliccinsa a yau Lahadi, 20 ga watan Satumba bayan ya shafe shekaru 45 kan mulki

Da yammacin yau Lahadi, 20 ga watan Satumba ne gawar Marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ta isa Zaria, inda za a gudanar da jana'izarsa da misalin karfe biyar na yamma.

An gano dandazon jama’a da suka taru domin jana’izar marigayin

Sarkin ya rasu ne a yau Lahadi, a asibitin sojoji na 44 da ke birnin Kaduna, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

Sarkin ya rasu yana da shekaru 84, ya kuma shafe shekaru 45 kan karagar mulki.

KU KARANTA KUMA: Zaben Edo: Abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da Gwamna Obaseki

Ga hotunan jana'izar nasa a kasa:

Hotunan yadda dandazon jama'a suka cika wajen jana'izar Sarkin Zazzau
Hotunan yadda dandazon jama'a suka cika wajen jana'izar Sarkin Zazzau Hoto: BBC
Asali: Twitter

Hotunan yadda dandazon jama'a suka cika wajen jana'izar Sarkin Zazzau
Hotunan yadda dandazon jama'a suka cika wajen jana'izar Sarkin Zazzau Hoto: BBC
Asali: Twitter

Hotunan yadda dandazon jama'a suka cika wajen jana'izar Sarkin Zazzau
Hotunan yadda dandazon jama'a suka cika wajen jana'izar Sarkin Zazzau Hoto: BBC
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Abubuwan da ya kamata ku sani game da Marigayi Sarkin Zazzau

Da farko mun kawo maku cewa Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya tabbatar da rasuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, bayan gajeriyar rashin lafiya. Sarkin ya rasu a asibitin sojoji na 44 da ke Kaduna a ranar Lahadi.

"Cike da alhini nake tabbatar da mutuwar baban jiharmu, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dr, Shehu Idris Idris," El-Rufai ya wallafa a Facebook.

Ya kara da cewa, "Ya rasu a asibtin sojoji na 44 da ke Kaduna a yau bayan gajeriyar rashin lafiya. Za a yi jana'izarsa a garin Zazzau da karfe 5 Insha Allah.

"Za a kiyaye dukkan dokokin dakile yaduwar annobar korona a yayin jana'izar da karbar makokinsa.

“Na sanar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan wannan babban rashin kuma yana mika ta'aziyyarsa.

"Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, zai jagoranci wakilan gwamnatin tarayya zuwa Zaria domin ta'aziyyar mai martaba a masarautar Zazzau da jihar Kaduna.

“Mun rasa babban abun alfaharinmu, mai cike da hikima sannan uban kowa. Allah ya bashi masauki a Aljanna Firdau. Amin"

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel