'Yan sanda sun cafke 'yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane 27

'Yan sanda sun cafke 'yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane 27

Rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa ta ce ta damke mutum 27 da ake zargi da laifin fashi da makami da kuma garkuwa da mutane a jihar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Bola Longe, ya sanar da manema a garin Lafia a ranar Litinin, cewa wadanda ake zargin an kama su ne a sassa daban-daban na jihar cikin makonni biyu.

A yayin kama wadanda ake zargin, Longe, a hedkwatar 'yan sanda da ke Lafia, ya ce daga cikinsu akwai wadanda ke da alaka da kisan dagacin kauyen Odu da ke karamar hukumar Nasarawa, Amos Obere, a ranar 31 ga watan Yuli.

Ya yi bayanin cewa, wadanda ake zarginsu da kisan dagacin an kama su ne a wata mashaya da ke birnin Nassarawa inda suke shagalinsu.

Ya ce wadanda ake zargin sun amsa laifinsu na garkuwa da mutane a kauyen Loko, wadanda ke kan hanyar zuwa Otukpo a jihar Binuwai daga Abuja, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce, akwai wadanda ake zargi da kisan wani jami'in hukumar shige da fice ta kasa mai mukamin sufirtandan, Salisu Usman Maku da kanwarsa Sa'adatu Usman Maku a Gudi da ke karamar hukumar Akwanga.

'Yan sanda sun cafke 'yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane 27
'Yan sanda sun cafke 'yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane 27. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotunan cikin gidan hamshakin mai kudin duniya da za a iya cire gidaje 18,000

Sauran wadanda ke a hannun 'yan sandan kamar yadda kwamishinan ya sanar, ya ce akwai wadanda ake zargi da garkuwa da Joseph Masin, shugaban kungiyar kiristoci ta kasa amma a reshen jihar.

Ya ce an samu bindigogi bakwai da harsasai tare da ababen hawa daga hannun masu laifin yayin da aka kama su.

Longe ya ce, "Rundunar na so ta tabbatar da cewa, ta shirya tsaf don tsare rayuka da kadarorin jama'ar jihar kuma hakan za ta bai wa fifiko saboda shine hakkinta.

"A saboda hakan, muna son tabbatar wa da jama'a cewa sai mun sauke hakkinmu

"'Yan sandan na son mika godiyarsu ga jama'ar gari, sarakunan gargajiya da dukkan sauran jami'an tsaro a kan goyon bayansu da muke samu, wanda hakan ya taimaka wurin nasarorinmu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel