Tuntuben aiki ya sa mu ka turawa Fasto Omale N573m a akawun – inji Banki

Tuntuben aiki ya sa mu ka turawa Fasto Omale N573m a akawun – inji Banki

Shugaban wani babban banki a Najeriya, ya ce Naira miliyan 573 da aka samu a akawun din Fasto Emmanuel Omale, sun shiga cikin asusun na sa ne da kuskure.

Manajan bankin ya fadawa kwamitin da ke binciken tsohon shugaban hukumar EFCC watau Ibrahim Magu wannan ne a lokacin da aka gayyace shi domin karin bayani.

Ya ce: “Bayan fitowar rahoton, mun gabatar da bincike kuma mun gano cewa an yi kuskure wajen kudin da aka tura, daga nan mu ka sanar da hukumar NFIU ta kasa.”

Kamar yadda jaridar The Cable ta fitar da rahoto a ranar Litinin, bankin ya ce an yi wannan kuskure ne sakamakon sauyin manhaja da su ka yi kwanakin baya.

A cewar shugaban bankin, yanzu sun rabu da manhajar Pinnacle-7 da ya jawo masu wannan tuntube, sun koma kan manhajar Pinnacle-10 wanda aka inganta aikinsa.

Ya ke bayani: “A lokuta da-dama, banki su kan sauya-sheka daga wannan manhaja zuwa wannan. Mu kan yi amfani da karshen mako ne wajen yin wannan aiki.”

KU KARANTA: EFCC: Ana sa ran kammala binciken da ake yi a kan Magu

Tuntuben aiki ya sa mu ka turawa Fasto Omale N573m a akawun – inji Banki
Ayo Salami ya na binciken Ibrahim Magu
Asali: UGC

“Sauyin-shekar ya na nufin dauke duk kudin masu hulda da bankin daga manhaja zuwa wata sabuwa. A dalilin wannan ne aka dauke asusun cocin Divine Hand Ministries.”

Emmanuel Omale shi ne babban Faston wannan coci na Divine Hand Ministries da ke kasar.

Manajan ya kara da cewa: “A wannan reshen banki na mu, mu na da asusu 983. Kudin da ke cikin duka wadannan asusu sun fada cikin akawun din cocin da ake magana.”

“An gano cewa an yi kuskuren jefa Naira miliyan 573 zuwa asusun Divine Hand Ministries.” Bankin ya gano hakan ne bayan tsawon lokaci.

A halin yanzu kwamitin da shugaban kasa ya kafa karkashin Ayo Salami ta na binciken Ibrahim Magu da laifuffukan da su ka hada da mallakar gidan Naira miliyan 573 a Dubai.

A baya Faston ya bayyana cewa bai saye wani gida da sunan Magu ba, amma ya tabbatar da ya taba ganawa da tsohon shugaban EFCC a kasar waje amma addu’a kadai ta hada su.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel