Cutar korona ta hallaka mutum 950 a Najeriya - NCDC

Cutar korona ta hallaka mutum 950 a Najeriya - NCDC

A halin yanzu an samu bullar cutar covid-19 a duk jihohi 36 na Najeriya da kuma babban birnin tarayya kamar yadda alkaluman cibiyar dakile yaduwar cututtuka a kasar NCDC suka tabbatar.

Babu shakka mahukunta na lafiya na ci gaba da aiki tukuru domin dakile yaduwar cutar a Najeriya, sai dai fa lamarin ya ci tura domin kuwa cutar na ci gaba da bazuwa babu sassauci.

Taskar bayanai ta NCDC a ranar Litinin, 9 ga watan Agustan 2020, ta ce cutar corona ta harbi mutane 46,867 yayin da mutum 33,346 suka samu waraka.

Ya zuwa yanzu dai mutane 950 cutar ta hallaka a fadin Najeriya kamar yadda hukumar NCDC ta fidda bayanan alkalumanta.

Shugaban hukumar NCDC; Chikwe Ihekweazu
Shugaban hukumar NCDC; Chikwe Ihekweazu
Asali: Twitter

Rumbun tattaro bayanai na NCDC ya nuna cewa, an yi wa mutum 319,851 gwajin cutar a duk fadin kasar tun bayan bullarta karo na farko a ranar 27 ga watan Fabrairun 2020.

Haka kuma alkaluman cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasar sun nuna cewa, mutum 12,571 ne suka rage masu dauke da kwayoyin cutar.

KARANTA KUMA: Ana iya yin jimami duk yadda aka ga dama idan na mutu - Obasanjo

Da misalin karfe 11.21 na jiya Litinin da daddare, NCDC ta sanar da cewa an gano karin sabbin mutane 290 da cutar ta harba a fadin Najeriya.

Sabbin mutane 290 da cutar ta harba cikin jihohi 16 sun kasance kamar haka:

Lagos (82), Plateau (82), Oyo (19), FCT (18), Edo (16), Kaduna (15), Enugu (9), Ogun (9), Kano (8), Kwara (8), Cross River (5), Ondo (5), Rivers (5), Ekiti (4), Imo (3) da Borno (2)

Har kawo yanzu jihar Legas ce a kan sahu na gaba ta fuskar yawan mutanen da cutar ta harba, sai kuma birnin Abuja a mataki na biyu yayin da jihar Oyo ta biyo bayansu a mataki na uku.

Ga jerin adadin mutanen da cutar ta hallaka cikin kowace daya daga cikin jihohi 36 na Najeriya da birnin Abuja da cutar ta bulla:

Lagos - 193

Abuja - 46

Oyo - 31

Edo - 100

Ribas - 54

Kano - 54

Kaduna - 12

Delta - 43

Filato - 22

Ogun - 24

Ondo - 28

Enugu - 19

Ebonyi - 26

Kwara - 21

Katsina - 24

Borno - 36

Abia - 5

Gombe - 23

Osun - 13

Bauchi - 14

Imo - 10

Benuwe - 9

Nasarawa - 8

Bayelsa - 21

Jigawa - 11

Akwa Ibom - 8

Neja - 12

Adamawa - 12

Ekiti - 2

Sakkwato - 16

Anambra - 18

Kebbi - 8

Zamfara - 5

Taraba - 4

Kuros Riba - 8

Yobe - 8

Kogi - 2

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel