'Canja Buratai, Sadique, Ekwe Ibas, ba shi zai kawo karshen matsalar tsaro ba'

'Canja Buratai, Sadique, Ekwe Ibas, ba shi zai kawo karshen matsalar tsaro ba'

Tsohon daraktan hukumar tsaro ta DSS, Mr Mike Ejiofor, ya yi tsokaci kan matsalolin tsaro da suka addabi wasu sassa daban daban na kasar. Ejiofor ya yi kira da a yi garambawul a fadin kasar, har ma da fannin tsaro ma damar ana son kawo karshen ta'addanci a kasar.

Tsohon daraktan hukumar tsaro ta DSS, Ejiofor a cikin shirin gidan talabijin na Channels ya ce canja hafsoshin tsaro ba zai kawo karshen matsalolin tsaro na kasar ba.

A cewarsa, mutum daya ne kawai ke da ikon canja hafsoshin tsaron, shine shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda shine oga kwata kwata a shuwagabannin tsaro.

Sai dai, a yayin da ya ke hakikance cewa hafsoshin na iya bakin kokarinsu wajen dakile wadannan matsaloli, a hannu daya kuma ya ce kokarin nasu ya kasa.

"Koda an canja hafsoshin tsaro a yanzu, a irin wannan yanayi na rashin tsaro, to bana tunanin akwai wani canji ko ci gaba da za a samu a wajen sabbin shuwagabannin.

"Rundunar soji da sauran jami'an tsaro basu da kayan aiki; akwai karancin ma'aikata a kowacce runduna ta tsaro. Da wannan annobar da ta kunno kai, lamura sun dagule," a cewarsa.

KARANTA WANNNA: Rundunar 'yan sanda ta ankarar da jama'a a kan sabon salon damfara da sunan COVID-19

'Chanja Buratai, Sadique, Ekwe Ibas, ba shi zai kawo karshen matsalar tsaro ba'
'Chanja Buratai, Sadique, Ekwe Ibas, ba shi zai kawo karshen matsalar tsaro ba'
Asali: UGC

Da yake ci gaba da jawabi, tsohon shugaban DSS din ya yi kira da samun hadin kan wasu kasashe don samun nasara akan yaki da ta'addanci, yana mai cewa Nigeria kadai ba za ta iya ba.

Ya yi nuni da cewa kasar Amurka ta tallafawa Nigeria da kayan aiki, ta hanyar bata jirgin yaki kirar Tucano da sauran kayan yaki, yana mai cewa jirgin zai dau lokaci kafin yazo.

Ejiofor ya yi kira da a yi garambawul a fadin kasar, ba wai a fannin gine gine ko rayuwar mutane ba, har ma da fannin tsaro ma damar ana son kawo karshen ta'addanci a kasar.

Ya yi wannan tsokacin ne a yayin da ake ci gaba da samun kiranye kiranye na hafsoshin tsaron suyi murabus ko kuma shi shugaban kasa ya tsige su da kansa.

Ko a baya bayan nan, majalisar tarayya ta kada kuri'ar rashin tabuka komai akan hafsoshin tsaro, inda ta bukaci Buhari ya tsigesu, ya sauya da wasu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel