Yadda wani masanin magunguna ya mutu yayin gasar lalata da karuwa a otel

Yadda wani masanin magunguna ya mutu yayin gasar lalata da karuwa a otel

Wani masannin kimiyyar hada magunguna ya yanke jiki ya mutu a lokacin da ya ke lalata da wata karuwa a wani otel da ke Igando a jihar Legas.

An gano gawar masanin magungunan, Bassey Asuquo a daya daga cikin dakunan otel din da ke kan titin Akesan, a unguwar Egan ta Igando a Legas a ranar Juma'a 31 ga watan Yuli.

Rahotanni sun ce Bassey da ake kyautata zaton shekarunsa sun kai arba'in, ya kama dakin otel din ne misalin karfe 10 na dare bayan ya sha giya a mashaya.

Wani mutum ya mutu a otel yayin lalata da karuwa
Wani mutum ya mutu a otel yayin lalata da karuwa. Hoto daga LIB
Asali: Twitter

Mahukunta otel din suka sanar da yan sanda da ke ofishin inda su kuma suka garzayo wurin da abin ya faru suka tarar da mutane da yawa sun taru domin leka gawar Bassey.

DUBA WANNAN: Kotu ta raba wasu ma'aurata saboda matar ba ta yarda mijin ya kusanci shimfidar ta

An tsinci sigari, da inhaler da gajeren wando a dakin amma ba a tarar da karuwar ba hakan ne nuna ta tsere abinta.

Wani rahoton ya ce karuwar da ta tsere ta kira manajan otel din a waya ta masa bayanin yadda numfashin marigayi Bassey ta rike sarkewa yayin da ya ke kokarin ciro maganinsa na inhaler kafin ya mutu.

An yi kokarin shawo kan ta domin ta dawo ta bayar da cikakken bayani amma hakan bai yiwu ba domin ta shaida wa manajan cewa tana dab da tsallake iyakar Najeriya ta tafi wata kasar don gudun kada a kama ta.

Yan sanda sun kama maaikatan otel din guda biyu yayin da ake dauke gawar aka tafi da ita dajin ajiye gawarwaki.

A bangarensu, iyalen mamacin suna can suna kokarin ganin yadda za a basu gawarsa domin su birne shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel