Jarumin fina-finan India, Amitabh Bachchan ya kamu da korona

Jarumin fina-finan India, Amitabh Bachchan ya kamu da korona

- Sannanen jarumin masana'antar Bollywood, Amitabh Bachchan, ya sanar da kamuwarsa da cutar korona

- Jarumin ya tabbatar da cewa an yi wa iyalansa da sauran hadimansa gwaji amma suna jiran sakamakon

- Jarumin mai shekaru 77 ya yi kira ga duk wanda ya san ya yi wata ma'amala da shi a cikin kwanaki 10 da suka gabata, da ya garzaya don gwaji

Fitaccen jarumin masana'antar Bollywood, wanda ya yi suna a duniya, Amitabh Bachchan, ya kamu da muguwar annobar nan da ta game duniya tare da zama ruwan dare.

Jarumin mai shekaru 77 ya kamu da cutar kuma an kwantar da shi a asibiti a ranar Asabar a garinsu na Mumbai.

Ya yi kira ga makusantansa da su garzaya don yin gwaji, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

"Na kamu da cutar korona kuma an mika ni asibiti," Bachchan ya rubuta yayin da yake sanar da cewa an yi wa iyalansa da hadimansa gwaji amma suna jiran sakamako.

"Duk wadanda suka kusanceni a kwanaki 10 da suka gabata, ina kira garesu da su garzaya don gwaji!" ya kara da cewa.

Jarumin fina-finan India, Amitabh Bachchan ya kamu da korona
Jarumin fina-finan India, Amitabh Bachchan ya kamu da korona. Hoto daga Channels TV
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zargin rufa-rufa: 'Yan daba sun kutsa ofishin NFIU, sun ragargaza kwamfutoci

A wani labari na daban, hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 575 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11.40 na daren ranar Juma'a 10 ga Yulin shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 575 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Lagos-224

Oyo-85

FCT-68

Rivers-49

Kaduna-39

Edo-31

Enugu-30

Delta-11

Niger-10

Katsina-9

Ebonyi-5

Gombe-3

Jigawa-3

Plateau-2

Nassarawa-2

Borno-2

Kano-1

Abia-1

31,323 ne jimmilan wadanda suka kamu

12,795 aka sallama kawo yanzu

709 sun mutu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel