Ibrahim Mustapha Magu ya koma kwana Masallaci a hannun yan sanda

Ibrahim Mustapha Magu ya koma kwana Masallaci a hannun yan sanda

- Dakatadtaccen shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya yi kwanansa na biyar a tsare

- Rahoto ya nuna cewa Magu ya koma kwana Masallaci yanzu a hedkwatar FCID

- Hukumar yan sanda Najeriya ta yi watsi da Magu saboda irin yadda yayi watsi da su a baya

Wani rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa mukaddashin shugaban hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC, Ibrahim Magu, ya daina kwana cikin ofishin yan sanda kamar yadda yayi kwanaki hudu da suka shude.

Magu, wanda ke fusktantar bincike gaban kwamitin fadar shugaban kasa karkashin Alkali Ayo Isa Salami, ya koma kwana a Masallacin dake cikin hedkwatar hukumar FCID.

An tattaro cewa an gyara ofishin FCID dake Zone 10, cikin birnin tarayya tun lokacin da aka tsare Magu a wajen.

Hakazalika, an tattaro cewa manya a hukumar yan sanda sun gana ranar Juma'a, 10 ga Yuli, domin tattaunawa kan lamarin Magu.

Rahoton yace manyan hukumar yan sanda sun yanke shawarar watsi da shi saboda rashin hadin kansa da hukumar yan sanda lokacin da yake cin mulkinsa a EFCC.

Majiyoyi daga hukumar sun bayyana cewa lokacin yake mulki, da gayya yake nunawa manyan yan sanda yatsa kuma ya daina halarta zamansu karkashin jagorancin IGP Adamu Muhammad.

Bugu da kari, an ruwaito cewa shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi ministoci da manyan jami'an gwamnati cewa kada su sake a gansu suna masu taimakawa Magu wannan lokacin.

Ibrahim Mustapha Magu ya koma kwana Masallaci a hannun yan sanda
Ibrahim Mustapha Magu ya koma kwana Masallaci a hannun yan sanda
Asali: UGC

Mun kawo muku rahoton cewa Lauyan Ibrahim Magu, a ranar Juma'a ya bukaci kwamitin fadar shugaban kasa dake bincike kansa ta bashi beli.

Ya ce akwai bukatar sakin Magu saboda yan jarida na amfani da damar tsareshi da akayi wajen wallafe-wallafen bata masa suna.

Ya kara da wasu bukatu shida daban.

Magu ya ce kwamitin na kira masu shaida kansa amma ba'a bari ya gansu balle amsa laifinsa ko kin amsawa.

Lauyansa, Mista Wahab Shittu, ya bayyana hakan ranar 10 ga Yuli, 2020.

KU KARANTA: Ibrahim Magu ya mika muhimman bukatu 7 ga kwamitin da ke bincikensa

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel