Ibrahim Magu ya mika muhimman bukatu 7 ga kwamitin da ke bincikensa

Ibrahim Magu ya mika muhimman bukatu 7 ga kwamitin da ke bincikensa

- Wasu sabbin tuhume-tuhume sun bayyana kan shugaban EFCC da aka dakatar

- Sifeto Janar na yan sanda ya janye dukkan jami'ansa dake gadin ofishin EFCC da Magu

Lauyan mukaddashin shugaban hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC da aka dakatar, Ibrahim Magu, a ranar Juma'a ya bukaci kwamitin fadar shugaban kasa dake bincike kansa ta bashi beli.

Ya ce akwai bukatar sakin Magu saboda yan jarida na amfani da damar tsareshi da akayi wajen wallafe-wallafen bata masa suna.

Ya kara da wasu bukatu shida daban.

Magu ya ce kwamitin na kira masu shaida kansa amma ba'a bari ya gansu balle amsa laifinsa ko kin amsawa.

Lauyansa, Mista Wahab Shittu, ya bayyana hakan ranar 10 ga Yuli, 2020.

Ibrahim Magu ya mika muhimman bukatu 7 ga kwamitin da ke bincikensa
Ibrahim Magu ya mika muhimman bukatu 7 ga kwamitin da ke bincikensa
Asali: UGC

Ga jerin bukatu 7 da ya mikawa kwamitin:

Wahab Shittu yace: "Bisa bayanan da mukayi, muna masu bukatar wadannan abubuwa da wurinka mai shari;a, da sauran mambobin kwamitin:

1. A baiwa mutuminmu (Magu) damar ganin manufar wannan kwamiti da abinda take niyyar yi

2. A nunawa abokinmu (Magu) takardun tuhume-tuhumen da ake yi masa domin bashi daman ganinsu, karantasu tare da shiryawa martani ko kare kansa

3. Abokinmu na bukatar taimakon wannan kwamiti domin a sakeshi daga hannun hukuma domin samun damar kare kansa sosai da kuma kula da lafiyarsa da ya fara samun matsala a tsare

KU KARANTA: Maimakon haska bidiyon karbar dalan Ganduje, da aikin da ka yiwa mutane ka haska - Ize-Iyamu ya caccaki Obaseki

4. A baiwa abokinmu isasshen lokaci bayani kan tuhume-tuhumen da ake yi masa tare da gabatar da hujjoji ga kwamitin nan.

5. A baiwa abokinmu damar gaba da gaba da wadanda suka shigar da kara kansa da hujjojinsa

6. Shaidu su gabatar da shaidarsu a gabansa

7. A baiwa abokinmu daman amsa laifinsa cikin tsanaki tare da hakkinsa na yanci yayin aikin wannan kwamiti

"Ya kai mai shari'a, shugaban kwamiti da mambobi, abokinmu zai yi matukar godiya idan kuka dau matakin wuri kan wadannan bukatu da ya mika a wasikar nan."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel