'Tsarin ya rage darajar albashinmu': ASUU ta koka da IPPIS

'Tsarin ya rage darajar albashinmu': ASUU ta koka da IPPIS

Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya (ASUU) ta ce tilasta mata shiga sabon tsarin biyan albashi na gwamnatin tarayya (IPPIS) ya tauye tare da rage darajar albashinsu.

Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi, ne ya sanar da hakan yayin da ya ke gabatar da jawabi a wurin taron bude wani dakin daukan darasi mai cin dalibai 1,000 da reshen kungiyar na jami'ar Jos ya gina.

ASUU ta gina tagwayen dakunan daukan darasin a kan miliyan N63.2 tare da sadaukar da su ga jami'ar Jos a matsayin wani bangare na aiyukan da ta saba yi domin inganta walwala (CSR)

Farfesa Ogunyemi ya bayyana cewa albashin malaman jami'o'i ya tsaya wuri guda ba tare da cigaba ba a tsawon shekaru 11 da su ka gabata, lamarin da ya ce ya jefa mambobinsu cikin 'tsanani da takura'.

Ya kara da cewa darajar albashin malaman jami'a kullun raguwa ta ke yi, hakan kuma ya na rage kwazonsu na aiki.

"Mamboinmu a takure su ke, su na cikin matsi, saboda albashinmu a tsaye ya ke a wuri guda a cikin shekaru 11 da su ka gabata.

"Sannan ga tilasta mana shiga tsarin IPPIS da aka yi, wanda yin hakan ya kara rage darajar kudin da ake biyan mambobinmu a matsayin albashi.

"Saboda darajar albashinmu ta na raguwa, kwazonmu na aiki ma raguwa ya ke, niyyarmu ta aiyukan agaji sai kara dusashewa ta ke yi," a cewar Ogunyemi.

'Tsarin ya rage darajar albashinmu': ASUU ta koka da IPPIS
Farfesa Ogunyemi
Asali: UGC

Shugaban na ASUU ya bukaci mambobinsu da karsu karaya, su cigaba da gwagwarmayar neman hanyoyin inganta jami'o'in Najeriya.

Jami'ar Bayero da ke Kano; wato BUK, ta mayar da wasu lakcarori bakin aikinsu bayan a baya ta sallamesu daga aiki saboda sabon tsarin biyan albashi (IPPIS) da gwamnatin tarayya ta bullo da shi.

Bayan gwamnatin tarayya ta tilasta malaman jami'o'i shiga tsarin IPPIS ne jami'ar BUK ta sallami lackcarorin daga aiki saboda su na aiki ne bisa tsarin kwangila.

DUBA WANNAN: 'Ka fara yin murabus kafin mu hadu a kotu'- Dan jarida ya mayarwa Osinbajo martani

Jami'o'i ne ke biyan lakcarorin da ke aiki a bisa tsarin kwangila daga kudaden aljihunsu.

IPPIS tsarin biyan albashi ne na ma'aikatan da gwamnatin tarayya ta dauka aiki kuma ta ke biyansu daga aljihunta, a saboda haka tsarin ba zai karbi ma su aiki bisa tsarin kwangila ba.

BUK ta sallami lakcarorin daga aiki a ranar 10 ga watan Yuni bayan gwamnatin tarayya ta kafe a kan cewa tilas sai dukkan malaman jami'o'in gwamnatin tarayya sun shiga tsarin IPPIS.

Daya daga cikin lakcarorin da aka sallama, Dakta Sa'idu Ahmad Dukawa, ya shaidawa jaridar HumAngle cewa jami'ar BUK ta kira shi kuma ta mayar da shi bakin aikinsa.

Ya bayyana cewa hukumar jami'ar ta kira shi ranar Litinin 2 sanna ta janye takardar gimtse aikinsa na kwangila da ta damka ma sa a baya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel