Shari'ar layin wayar Hanan Buhari: Kotu ta yi fatali da karar DSS

Shari'ar layin wayar Hanan Buhari: Kotu ta yi fatali da karar DSS

- Kotu taki amincewa da bukatar gudun biyan diyyar Naira miliyan 10 da Hukumar DSS ta shigar dangane da shari'ar da ake ci gaba da yi kan layin wayar Hanan Buhari

- Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a birnin Asaba na jihar Delta, ta ce ba ta da hurumin sauraron karar a yanzu

- Alkalin kotun, ya ce an shigar da kara a Kotun daukaka kara wacce a yanzu ita ke da ikon sauraron karar

Kokarin da Hukumar 'Yan Sandan Farin Kaya ta DSS ta ke yi domin kin biyan diyyar Naira miliyan 10 da aka shimfida mata saboda tsare Anthony Okolie ba bisa ka’ida ba, bai yi nasara ba gaban kotu.

Babbar Kotun Tarayya ta yi watsi da bukatar da Hukumar DSS ta gabatar mata ta neman kauce wa biyan diyyar Naira miliyan 10 saboda tsare Mista Okolie har na tsawon makonni goma.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, Hukumar DSS ta shigar da bukatar ne a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Asaba, babban birnin jihar Delta.

Shugaban Hukumar DSS; Hanan Buhari da Mista Anthony Okolie
Shugaban Hukumar DSS; Hanan Buhari da Mista Anthony Okolie
Asali: Twitter

Idan ba ku manta ba, a watan Yulin 2019 ne Hukumar DSS ta cafke Mista Okolie saboda saye da yin amfani da tsohon layin wayar Hanan Buhari, ‘yar Shugaba Muhammadu Buhari.

Bayan sakin Mista Okolie, ya maka Hukumar DSS da kamfanin Layin wayar da kuma 'yar shugaban kasar a kotu, inda ya nemi a biya shi diyyar tauye masa hakkin da aka yi.

A sanadiyar haka ne kotun ta yi riko da bukatar da Mista Okolie ya shigar, inda ta umarci Hukumar DSS ta biya shi diyyar naira miliyan 10 sakamakon tauye masa hakkin da ta yi.

KARANTA KUMA: Osinbajo ya jagoranci gwamnoni 36 a zaman majalisar tattalin arziki

Sai dai har kawo yanzu, Hukumar bata yi wa umarnin kotun biyayya ba, inda Lauyan Mista Okolie ya yi barazanar sake maka Hukumar a kotu tun da ta yi biris da umarnin kotun.

Ana cikin haka ne kuma sai Hukumar DSS ta sake shigar da kara, inda ta nemi kotun ta dakatar da Okolie daga tirsasa mata biyan shi diyyar naira milyan 10 da ya bukata.

Sai dai kotun ta yi fatali da karar tare da bayyana dalilin cewa, ba ta da hurumin sauraron karar domin kuwa an riga da shigar da karar a gaban kotun daukaka kara, saboda haka ita ce mai wuka da nama a yanzu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel