Yanzu-yanzu: An kirkiri sabon na'urar gwajin cutar Korona a Najeriya

Yanzu-yanzu: An kirkiri sabon na'urar gwajin cutar Korona a Najeriya

A yau Alhamis, 9 ga 2020, gwamnatin tarayyar Najeriya ta kaddamar da sabon na'urar gano abinda ke janyo cutar Coronavirus mai suna RNASwift, Daily Trust ta ruwaito.

Masana Kimiyan Najeriya ne suka kirkiri wannan na'ura.

Mukaddashin shugaban hukumar cigabar ilmin fasahar Biotechnology wato NABDA, Farfesa Alex Akpa, wanda ma'aikatarshi ce ta kirkira na'urar ya ce wannan zai taimaka matuka wajen kara adadin gwajin cutar COVID-19.

Ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da na'urar yau a Abuja.

Farfesa Alex Akpa yace: "Wannan na'ura ya keta raini a ilmin Biotechnolgy, wanda aka yi amfani da ilmin Biology wajen ginashi cikin farashi mai sauki amma mai matukar kyau wajen gwajin cutar covid-19."

Saurari cikakken rahoton...

Asali: Legit.ng

Online view pixel