Yanzu-yanzu: An yi garkuwa da babban alkali

Yanzu-yanzu: An yi garkuwa da babban alkali

- Masu garkuwa da mutane sun sace Mai shari'a Donatus Yantau Shidda a jihar Taraba

- An sace babban alkalin ne a safiyar yau Litinin

- Shidda na tare da matarsa a yayin da 'yan bindigar suka isa gidansa da ke yankin Kona a Jalingo

'Yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban kotun gargajiya, Mai shari'a Donatus Yantau Shidda a jihar Taraba.

An sace babban alkalin ne a safiyar yau Litinin a jihar Taraba.

Wata majiya daga iyalansa ta ce Shidda na tare da matarsa a yayin da 'yan bindigar suka isa gidansa da ke yankin Kona a Jalingo.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A wani labarin kuma, mun ji cewa Hamisu Bala, mutumin da ake zargi da zama mashahurin mai garkuwa da mutane ya gurfana a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a kan zarginsa da ake da laifin ta'addanci.

Yunkurin kama Wadume ya janyo rasa rayukan 'yan sanda uku tare da farar hula daya a jihar Taraba. Amma kuma 'yan sanda sun damke Wadume a watan Augusta na shekarar 2019.

A watan Fabrairu da ya gabata, sifeta janar din 'yan sanda ya mika laifuka 16 gaban kotu da ake zargin Wadume da su wadanda suka hada da ta'addanci.

Amma kuma ofishin Antoni janar din tarayya ya karba gabatar da karar. An rage zargin zuwa 12 daga 16 na farko. An sake rage wadanda ake zargin daga 20 zuwa mutane 7.

Ana zargin Wadume da wadannan laifukan ne tare da Aliyu Dadje (Sifetan dan sanda), Auwalu Bala wanda aka fi sani da omo razor, Uba Bala wanda aka fi sani da Uba Delu, Bashir Waziri wanda aka fi sani da Baba runs, Zubairu Abdullahi wanda aka fi sani da Basho da kuma Rayyanu Abdul.

Dukkan wadanda ake zargin sun ki amsa laifuka 12 da ake zargin su da shi da suka hada da "ta'addanci, garkuwa da mutane, ci gaba da tsarewa da kuma karbar miliyan 106."

Lauyan Wadume T. Dangana, ya sanar da kotu cewa har yanzu ba a ce komai ba a kan bukatar belin da ya mika gaban kotu ba kuma wanda yake karewa na farko yana fama da matsanancin rashin lafiya don ko tari yayi, jini ke fita daga bakinsa.

Shuaibu Lawan, babban lauya daga ma'aikatar shari'a, ya ce ba za a duba bukatar belin ba don ta dogara ne a kan laifukan farko.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel