Siyasa mugun wasa: An yi ma wani Kansila zigidir a jahar Zamfara

Siyasa mugun wasa: An yi ma wani Kansila zigidir a jahar Zamfara

Kansila dake wakiltar mazabar Galadama-Dangaladima a majalisar karamar hukumar Kaura-Namoda ta jahar Zamfara, Sagir Dansani ya ci dukan tsiya sa’annan aka masa tsirara.

Punch ta ruwaito kansilan ya bayyana haka ne daga gadon asibitin da yake jinya a garin Kaura Namoda, inda yace wasu miyagu ne suka dauke shi daga gidansa a ranar Asabar.

KU KARANTA: Yansanda sun dirka ma matashi bindiga yayin da yake yin alwala a kofar gida

“Ba su tsaya ko ina ba sai sakatariyar karamar hukumar inda suka lakada min dan banzan duka, har sai da na fita hayyaci na.

"koda na farfado, sai na tarar dani a tsirara haihuwar uwata, daga nan na shiga kuwwa ina neman taimako, shi ne aka garzaya da ni babban asibitin Kaura Namoda.” Inji shi.

Siyasa mugun wasa: An yi ma wani Kansila zigidir a jahar Zamfara
Gwamnan jahar Zamfara
Asali: Twitter

Sai dai Sagir ya zargi shugaban karamar hukumar, Alhaji Lawali Abdullahi da shirya masa wannan tuggun saboda kawai a cewarsa ba sa cikin jam’iyya daya.

Sagir ya kara da cewa yayin da ake dukansa, ya ji guda daga cikin miyagun yan cewa sai sun koya masa hankali tun da har ya fara kalubalantar shugaban karamar hukumar.

A cewarsa, ya fara samun matsala ne tun bayan da ya ki komawa jam’iyyar PDP tare da shugaban karamar hukumar a lokacin da Gwamna Bello Matawalle ya zama gwamna.

Hakan bai yi ma shugaban karamar hukumar dadi ba, don haka ya tsane shi tare da sauran kansilolin dake cikin jam’iyyar APC, kuma ciyaman din ya rike musu alawus dinsu na wata 3.

Amma da aka tuntubi ciyaman Abdullahi game da lamarin, sai ya musanta wata masaniya, kuma yace ta yaya zai sa a aikata wannan danyen aiki a cikin sakatariyar karamar hukumar?

“Allah ne shaida na, ban san komi ba game da wannan lamarin, kuma tuni na sa jami’an tsaro su binciko wadanda suka tafka masa wannan danyen aikin domin su fuskanci fushin doka.” Inji shi.

Sauran mutanen da harin ya shafa, kuma suka jikkata a sanadiyyar haka sun hada da Mubarak Bello, Yakubu Sani, Ibrahim Ahmad da Alhaji Lawal Mohammad.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel