Shugaba Buhari ya nada Farfesa Obioma a matsayin sabon shugaban Hukumar NECO

Shugaba Buhari ya nada Farfesa Obioma a matsayin sabon shugaban Hukumar NECO

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Farfesa Godswill Obioma, a matsayin sabon shugaban hukumar shirya jarrabawar kammala karatun sakandire ta kasa, NECO.

Gabanin wannan sabon nadi, Farfesa Obioma ya kasance Kwamishinan hukumar zabe ta kasa mai zamanta INEC reshen jihar Ebonyi.

Wannan rahoto yana kunshe ne cikin wata sanarawa da babban jami'in hulda da al'umma na Hukumar NECO, Azeez Sani ya fitar a ranar Juma'a, 22 ga watan Mayu.

Sanarwar nadin mukamin Farfesa Obioma na kunshe ne cikin wata wasika mai lamba FME/PS/396/C1/1/134 da kwanan watan 15 ga watan Mayu, wadda Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya rattaba wa hannu.

Wasikar Ministan ta bayyana cewa, kujerar Farfesa Obioma za ta fara aiki ne daga ranar 14 ga watan Mayu, har zuwa tsawon wa'adin shekaru biyar.

Sabon shugaban Hukumar NECO; Farfesa Godswill Obioma
Sabon shugaban Hukumar NECO; Farfesa Godswill Obioma
Asali: UGC

KARANTA KUMA: Matawalle ya ware N60m saboda gasar addinin musulunci ta bana a Zamfara

An haifi Farfesa Obioma a ranar 12 ga watan Dasumba na shekarar 1953, kuma ya fito daga karamar hukumar Bende ta jihar Abia.

Farfesa Obioma wanda ya karbi ragamar Hukumar NECO a ranar Juma'a a babban ofishinta da ke birnin Minna na jihar Neja, ya maye gurbin mukaddashin shugaban hukumar, Mallam Abubakar Gana.

Ya kasance tsohon babban sakataren Cibiyar Nazari da Binciken Ci gaban Ilimi ta kasa, NERDC.

Ya rike kujerar Darekta a Ma'aikatun Ilimi daban-daban da suka hada da; Hukumar NABTEB, UBEC, NPEC, da kuma Shugaban sashen ilimin kimiya a Jami'ar Jos ta jihar Filato.

A makon da ya gabata ne shugaba Buhari ya amince da sallamar tsohon shugaban hukumar NECO, Farfesa Charles Uwake, da wasu jami'an hukumar hudu sanadiyar kama su da laifuka masu nasaba da almundahana.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, gabanin tsige Farfesa Uwake a ranar Juma'ar da ta gabata, an dakatar da shi na tsawon shekaru biyu yayin da ake ci gaba da bincike kan laifukan da ake zarginsa da aikatawa.

Sauran manyan jami'an hukumar da aka kora tare da shugaban sune; Mista Bamidele Olure (darektan kudi da asusu), Dakta Shina Adetona (shugaban sashen harkokin kwangila), Mista Tayo Odukoya (mataimakin darekta) da Barista Babatunde Aina (shugaban bangaren shari'a).

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel