Boko Haram: Hotunan 'yan ta'adda 20 da dakarun Najeriya suka halaka

Boko Haram: Hotunan 'yan ta'adda 20 da dakarun Najeriya suka halaka

A ruwan wutar da dakarun bataliya ta 130 da ke aiki a babban sansanin soji da ke Baga suka yi wa 'yan ta'adda, sun yi nasarar halaka mayakan Boko Haram da ISWAP 20 a ranar 17 ga watan Mayu.

'Yan ta'addan sun bayyana dauke da makamai inda suka nufi wasu kauyuka da ke Baga.

Tawagar dakarun sojin sun tare 'yan ta'addan inda suka ragargaza su tare da kashe 20 daga ciki har lahira.

Kamar yadda hedkwatar tsaro ta kasa ta bayyana, dakarun sun samu nasarar kwace bindigogi kirar AK 47 shida, harsasai na musamman har 520 da kuma gwafa 36.

Amma kuma, wasu daga cikin zakakuran dakarun sun samu raunika amma babu rai da aka rasa. Da gaggawa aka kwashe su zuwa sashe na 3 na asibitin sojin don samun taimakon likitoci.

Shugaban rundunar sojin Najeriya, Tukur Buratai ya jinjinawa dakarun ta yadda suka nuna kwarewarsu.

KU KARANTA KUMA: Rikicin kabilanci: Fintiri ya saka dokar ta-baci a karamar hukumar Lamurde

Ya shawarcesu da su mayar da hankali wajen kawo karshen ta'addancin kwata-kwata a yankin arewa maso gabas.

Hedkwatar tsaron ta wallafa a shafinta na twitter cewa: “Rundunar Operation Lafiya Dole ta kashe yan ta’addan Boko Haram/ISWAP a Baga, jihar Borno.

"A wani arangama da suka yi, dakarun bataliyan 130 tare da taimakon babban sansanin soji na Baga, sun fafata a arewa maso yamma."

A wani labarin na daban, mun ji cewa wani gwamna a kasar Somaila Ahmed Muse Nur tare da masu gadinsa sun rigamu gidan gaskiya a sanadiyyar wani harin kunar bakin wake da aka kai musu a ranar Lahadi.

Kamfanin dillancin labarun AFP ta ruwaito lamarin ya faru ne a birnin Galkayo, yayin da Ahmed, wamnan lardin Mudug ta Arewa ta tsakiya ke cikin tafiya a ayarin motocinsa.

Dan kunar bakin wake a cikin scooter ne ya buga ma ayarin motocin gwamnan, daga nan ya tashin bamabaman da yayi jidiga dasu, nan take gwamnan, direbansa da masu gadi suka mutu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel