COVID-19: Kano na cikin mawuyacin hali - Ganduje

COVID-19: Kano na cikin mawuyacin hali - Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce akwai babbar matsala a jihar Kano sakamakon bullowar cutar coronavirus.

A yayin gabatar da dakin gwaji na tafi-da-gidanka da gidauniyar Dangote ta baiwa jihar kyauta a ranar Lahadi, Ganduje yace jinkirin gwaji ne ke kawo karuwar cutar a jihar.

Kamar yadda takardar da sakataren yada labarai na gwamnan jihar, Abba Anwar ya gabatar, ya ce rashin isassun dakunan gwaji a jihar ne yasa annobar ke kara tsananta.

Ganduje yace, "Babu shakka jihar Kano na cikin babbar matsala. Babu shakka mun fara gidauniya mai amfani. A da muna daukar sa'o'i 7 kafin samfur ya kai Abuja kuma yana daukar sa'o'i 7 kafin a dawo da shi.

COVID-19: Kano na cikin mawuyacin hali - Ganduje
COVID-19: Kano na cikin mawuyacin hali - Ganduje
Asali: Twitter

"Mun mika koken mu ga shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya yi umarnin a samar da dakin gwaji a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano.

"Ya dauka kwanaki yana aiki amma sai ya tsaya, lamarin ya kawo hauhawar cutar a jihar.

"Amma bayan dawowar aikin dakin gwajin da kuma samun karuwar na jami'ar Bayero, Kano tana gwada samfur 200 a kowacce rana.

"Da samun karuwar dakin gwaji na gidauniyar Dangote mai iya gwada samfur 400, mun fara bude hanyar shawo kan matsalar."

Shugaban hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya, Dr Chikwe Ihekweazu ya samu halartar taron.

A cewar shugaban, "Ina so jama'ar jihar Kano su san cewa bamu manta dasu ba, muna tare dasu dari bisa dari.

KUKARANTA KUMA: Kwamishinan Bauchi ya bayyana ainahin maganin da suka yi amfani da shi wajen warkar da masu COVID-19 a jahar

"Ina son tabbatar muku da cewa, bayan mun samu sakamakon binciken Dr Nasiru Sani Gwarzo na kwamitin yaki da cutar na fadar shugaban kasa, za mu yi amfani da shi don kawo karshen al'amarin da ke faruwa a Kano."

Kamar yadda NCDC ta bayyana, mutum 329 ne suka kamu da muguwar cutar a jihar Kano.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel