Sakamakon gwajin mutane 90 da ke nuna alamun COVID-19 a Abuja ya fito, basa dauke da cutar

Sakamakon gwajin mutane 90 da ke nuna alamun COVID-19 a Abuja ya fito, basa dauke da cutar

Hukumar babbar birnin tarayya, ta ce sakamakon gwaji ya nuna cewa mutane 90, wadanda suka nuna alamun cutar COVID-19, basa dauke da cutar.

Hukumar birnin ta bayyana hakan ne a shafinta na twitter, inda ta yi bayanin cewa wadanda aka yiwa gwajin sun fito ne daga garin Mpape da ke Abuja.

Ta ce a lokacin “binciken zakulo wadanda suka kamu ne”, ma’aikatar lafiyarta ta gano mutanen sannan ta yi masu gwaji, inda sakamakon ya nuna basa dauke da cutar.

“Yayinda FCTA ke ci gaba da binciken masu cutar a garuruwan Abuja, sakamakon mutane 90 daga yankin Mpape ya fito, kuma duk basa dauke da COVID-19,” ta wallafa a shafin nata.

Ta kara da cewa a aikin binciken, “za a tantance duk wanda ke da tarihi na tari, zazzabi, mura, ciwon kirji da wahala wajen numfani.

“Za a yi hakan ne domin gano duk wanda ke dauke da cutar COVID-19 da kuma basu kulawar da ya kamata a kan lokaci domin tsinke igiyar yaduwar cutar a birnin tarayya.”

KU KARANTA KUMA: Tallafi 17 da Gwamnatin tarayya ta samu domin yaki da cutar COVID-19

A wani labarin, shugaban cibiyar kula da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC), Dr Chikwe Ihekweazu, ya yi amanna cewa kowace jaha a Najeriya za ta samu kasonta na annobar coronavirus.

Ihekweazu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya bayyana a shirin safe na Channels TV wato Sunrise Daily.

Ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya na kokarin ganin ta hana cutar yaduwa, inda ya ce hakan ya kasance babban aiki mai matukar wahala.

Ya kuma yi martani kan banbanci da aka samu a yawan adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 da NCDC ta saki, da kuma adadin a wasu jihohi, musamman a Lagas da Kano.

Dr Ihekweazu ya bayyana cewa hukumar lafiyar na ta aiki domin magance coronavirus, yayinda hukumomin jihohi na da nasu rawar ganin da za su taka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel