COVID-19: Ministan Buhari ya yi bayanin yadda rayuwarsa ke tafiya yayin annobar

COVID-19: Ministan Buhari ya yi bayanin yadda rayuwarsa ke tafiya yayin annobar

- Ministan sufurin jiragen sama kuma dan kwamitin shugaban kasa na yaki da cutar coronavirus ya bayyana yadda rayuwar shi ta kasance a yayin aiki

- Kamar yadda Hadi Sirika ya bayyana, wannan aikin ya karbeshi ne da zuciya daya tare da fatan sauke nauyin kasar shi da aka daura mishi

- Ya ce baya tsoron kamuwa da cutar don ba lasisin mutuwa bace kuma ko an mutu shahada ce

Ministan sufurin jiragen sama kuma dan kwamitin shugaban kasa na yaki da cutar coronavirus, Hadi Sirika, ya sanar da jaridar Daily Trust yadda yake sauke nauyin da ke kanshi a yayin da ake fama da cutar coronavirus.

Ya sanar da wakilin jaridar Daily Trust cewa ya saka a ranshi cewa zai bautawa jama'a ne shiyasa ya karba aikin. Zai jure tare da jajircewa wajen taimakon kasarsa.

COVID-19: Ministan Buhari ya yi bayanin yadda rayuwarshi ke tafiya yayin annobar
COVID-19: Ministan Buhari ya yi bayanin yadda rayuwarshi ke tafiya yayin annobar
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: An sako shahararren dan wasan kwallon kafa Ronaldinho daga gidan yari

"A kuma lokutan da ayyuka suka tsananta, ina daukar mintoci don karanta Qur'ani. Ina kuma amfani da wannan damar wajen jawo hankulan yarana kanana don ina da guda biyu. Na kan fita hawan doki."

Ya kara da cewa, wadannan ne abubuwan da nake yi don hutawa. Amma kuma bayan na yi sallar asuba, na kan dau mintoci don motsa jiki. Gaskiya mai aikin jama'a bai cika samun lokacin kanshi ba," Sirika yace.

A lokacin da aka tambayeshi ko akwai lokutan da yake tunanin zai iya kwasar kwayar cutar, ya ce cutar ba lasisin mutuwa bace. A don haka baya tsoron samunta.

Ya ce, "Idan an kaddara min samun cutar coronavirus, zan sameta kuma ba lasisin mutuwa bace. An sanar da mu cewa mu dinga wanke hannayenmu tare da gujewa shiga taro."

Ya kara da cewa, "muna yin iyakar bakin kokarinmu amma za mu iya samunta. Amma akwai magani kuma ana warkewa. Wadanda suka samu suna zama asibiti a killace, kuma suna komawa cikin iyalansu."

"Idan na kamu da cutar, zan je asibiti kuma zan warke. Idan kuwa ta zama ajalina, na san shahada nayi don annoba ce," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel