Dakarun sojin Najeriya sun dakile harin Boko Haram a Borno, sun kashe mutum 2 sannan suka kwato motar bindiga

Dakarun sojin Najeriya sun dakile harin Boko Haram a Borno, sun kashe mutum 2 sannan suka kwato motar bindiga

- Rundunar sojojin Najeriya na ci gaba da yin gagarumin nasara a arewa maso gabas

- Dakarun sojin a babban sansaninsu na Gamborua jahar Borno sun yi jarumta a wani hari da yan ta’addan Boko Haram suka kai yankin

- Sojojin sun dakile harin yan ta’addana sannan suka kashe biyu a cikinsu, da kuma kwato motar bindigar da yan ta’addan suka yi amfani da shi

`Dakarun sojojin Najeriya na bataliya ta 3 a babban sansanin soji na 11 Gomboru da ke jahar Borno sun dakile wani harin da yan ta’addan Boko Haram/ISWAP suka yi yunkurin kai wa.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mukaddashin daraktan ayyukan labarai na tsaro, Birgediya Janar Benard Onyeuko ya aike wa manema labarai a ranar Laraba, 6 ga watan Afrilu.

A cewar jawabin, dakarun dun kuma yi arangama da wasu mayakan Boko Haram/ISWAP a cikin wasu manyan motocin bindiga guda bakwai da Babura da yawa, inda suka tunkari wajen bataliyan da misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Talata, 7 ga watan Afrilu.

Dakarun sojin Najeriya sun dakile harin Boko Haram a Borno, sun kashe mutum 2 sannan suka kwato motar bindiga
Dakarun sojin Najeriya sun dakile harin Boko Haram a Borno, sun kashe mutum 2 sannan suka kwato motar bindiga
Asali: Facebook

Sai dai an sha kan yan ta’addan inda daga bisani suka ci na kare. Dakarun sojin sun fatattake su har zuwa yankin Wurge.

Musayar wutar da suka yi, ya yi sanadiyar mutuwar yan ta’adda biyu da kumajikkata wasu da ba a tabbatar da adadinsu ba.

Bugu da kari, dakarun sun kwato manyan motocin bindiga guda 3, bindigun jirgin sama 2, AK 47 guda 2, bindigar HK 21 guda 1 da yan ta’addan suka zubar.

Sauran kayayyakin da suka samo sun hada da harsashin 1.5 M M guda 10, mujjala guda 2 da lasifika da wakar nasarar yan Boko Haram.

KU KARANTA KUMA: Matasa sun yi zanga-zanga a Kaduna kan kisan wasu mutane 5

Babu sojan da ya rasa ransa ko ya ji rauni kuma sojoji basu rasa kayayyakinsu ba a arangamar.

A gefe guda mun ji cewa mayakan ƙungiyar Boko Haram suna nan sun kai hari a garin Ngala da ke jihar Borno kamar yadda Sahara Reporters ta tabbatar.

Wannan harin yana zuwa ne kasa da awa 24 da harin da yan ta'addan suka kai a Kirchinga a karamar hukumar Madagali na jihar Adamawa a daren ranar Litinin inda suka kone gidaje fiye da biyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel