Da duminsa: An damke wanda ake zargi da kisan mataimakiyar diraktar fadar shugaban kasa

Da duminsa: An damke wanda ake zargi da kisan mataimakiyar diraktar fadar shugaban kasa

Jami'an yan sanda a Abuja sun damke wani wanda ake zargi da laifin kisan mataimakiyar diraktar fadar shugaban kasa, Laetitia Dagan, a ranar Litinin.

A cewar kakakin hukumar yan sandan birnin tarayya Abuja, Anjuguri Manza, ya ce an damke mutumin sakamakon binciken da aka kaddamar kan lamarin.

Ya kara da cewa mutumin wanda aka sakaye suna da fuskarsa don manufar bincike ya aikata aika-aikan ne tare da wasu abokansu kuma ana nemansu.

Da duminsa: An damke wanda ake zargi da kisan mataimakiyar diraktar fadar shugaban kasa
Da duminsa: An damke wanda ake zargi da kisan mataimakiyar diraktar fadar shugaban kasa
Asali: UGC

KU KARANTA: EFCC ta dakile yunkurin shigar wa da mai laifi miyagun kwayoyi

Mun kawo muku rahoton cewa wasu makasa sun hallaka mataimakiyar diraktar gudanarwan fadar shugaban kasa, Laetitia Dagan, a gidanta dake Abua, fadar shugaban kasa ta bayyana.

Mataimakin dirkatan labaran fadar shugaban kasa, Attah Esa, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya sake inda ya ce an kashe Dagan ne misalin karfe 11 na daren Litinin.

Attah Esa ya bayyana cewa babbar ma'aikaciyar fadar shugaban kasan ta yi aiki a ofishinta zuwa misalin karfe takwas na dare amma zuwa 11 aka samu labarin kisan gillan da akayi mata.

Sakataren din-din-din fadar shugaban kasa, Jalal Arabi, wanda ya kai gaisuwar ta'aziyya ga iyalan maragayiyar ya siffanta a matsayin ma'aikaciya mai jajircewa na gaske.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel