Muna bukatar karin sojoji 100,000 domin cin galaba a kan Boko Haram - Zulum

Muna bukatar karin sojoji 100,000 domin cin galaba a kan Boko Haram - Zulum

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce Najeriya na bukatar karin sojoji 100,000 domin cin galaba a kan 'yan kungiyar ta'addan Boko Haram.

Ya bayar da shawarar cewa a dauki a kalla mutane 50,000 aikin soja daga jihar Borno domin su tallafa wurin yaki da ta'addancin ko suna da karatun boko ko ba su da shi.

Zulum ya yi wannan jawabin ne yayin da ya karbi bakuncin tawagar kwamitin tsaro na majalisar wakilan tarayya a ranar Laraba karkashin jagorancin Hon. Babajimi Benson.

Gwamnan ya jadadda cewa ba za a iya cin nasara a yaki da 'yan ta'addan ba sai an samu isasun sojoji da fasaha da kudi.

Muna bukatar karin sojoji 100,000 domin cin galaba a kan Boko Haram - Zulum
Muna bukatar karin sojoji 100,000 domin cin galaba a kan Boko Haram - Zulum
Asali: Facebook

Zulum ya shaidawa Benson yayin ziyarar sa cewa "ba za ka iya kawo karshen ta'addanci ba idan ba ka da makamai da fasahar zamani da isasun kudi."

Ya ce, "Rundunar soji ba ta da isasun dakaru, ba su da kayan aiki. Ku shawarci Kakakin majalisa da Shugaban Majalisar Dattawa su fada wa Shugaban kasa ya bayar da umurnin daukan sabbin sojoji. Mu na bukatar a kalla sojoji 100,000. Su zo su dauki 'yan asalin jihar Borno aikin soja ko suna da karatun boko ko ba su da shi.

"Muna bukatar daukan a kalla mutane 50,000 daga Borno, muna da jaruman maza da za su iya shiga aikin soja ko da na wucin gadi ne."

Benson ya sanar da gwamnan cewa shi da kwamitinsa sun zo Maiduguri ne domin yi masa ta'aziyyar mutanen da suka rasu a harin Auno.

Benson ya kara da cewa kwamitin kuma ta zo jihar ne domin su ga abinda za su iya yi domin taimakawa a yakin da suke yi da ta'addanci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel