Rusau: Gwamnati ta rushe kasuwar waya ta Maiduguri (Hotuna)

Rusau: Gwamnati ta rushe kasuwar waya ta Maiduguri (Hotuna)

Jami'an tsaro sun hana masu tebura da shaguna shigar kasuwar masu kasuwancin wayoyin hannu da kayan amfaninsu yayin da ake shirin rushe kasuwar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

An kai manyan motocin rusau bakin kasuwar, yayin da jami'an tsaro suka raba kansu a kusurwoyin kasuwar gabanin fara rusau din.

Matasa, cikin yanayi fushi da damuwa, sun tsaya daga gefe suna kallon yadda ake baje tebura da shagunan kasuwar da aka fi kira da 'kasuwar Jagwal'.

DUBA WANNAN: An bayyana abinda cire su Buratai zai haifar a Najeriya

Da yawa daga cikin 'yan kasuwar da manema labarai suka tattauna da su sun bayyana cewa basu da masaniya a kan dalilin da yasa aka rufe hanyoyin da ke sada jama'a da kasuwar.

Rusau: Gwamnati ta rushe kasuwar waya ta Maiduguri (Hotuna)
Kasuwar waya ta Maiduguri
Asali: Twitter

Rusau: Gwamnati ta rushe kasuwar waya ta Maiduguri (Hotuna)
Rusau: Gwamnati ta rushe kasuwar waya ta Maiduguri
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel